Mai juna-biyu ta mutu a wajen zaɓe a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau.

Wata mata mai juna-biyu mai suna Shamsiya Ibrahim ta yanke jiki ta faɗi matacciya a yayin da take jiran layin kaɗa ƙuri’a yayin zaɓen Shugaban Ƙasa da na ‘yan Majalisar Tarayya.

Wannan al’amari ya auku ne ranar Asabar a yankin ƙaramar hukumar Tsafe da ke Jihar.

Blueprint Manhaja ta tattaro cewa bayan da matar ta yanke jiki ta faɗi, an garzaya da ita Babban Asibitin Tsafe inda aka tabbatar da rasuwarta.

Shamsiya ta yi tattaki ne daga yankin Kotorkoshi da ke Ƙaramar Hukumar Bunguɗu zuwa garin Tsafe mai nisan kimanin kilomita 50 don kaɗa ƙuri’arta.

Mutuwar Shamsiya ta girgiza masu kaɗa ƙuri’a a rumfar zaɓen wanda ya yi sanadiyar wasu suka fasa zaɓen saboda jimamin rasuwar.

Wata ‘yar uwar marigayiyar mai suna Aisha Muhammad, ta ce kwanan ‘yaru warta biyu ba ta da lafiya, amma duk da haka ta daure ta je gurin kaɗa kuri’ar.

Ta ce, “Haƙiƙa duk mai rai mamaci ne, ashe ‘yar uwata a wajan zaɓe ne Allah Ya yi sanadiyar rasuwarta ɗauke da juna-biyu. Allah Ya jiƙan ta da rahama, amin.”

Ya zuwa haɗa wannan labari babu wata sanarwa a hukumance game da batun.