Tinubu ya lallasa Obi a rumfar zaɓen Obasanjo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar Labour, Peter Obi ya sha kaye a rumfar zaɓe ta tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo a zaɓen Shugaban Ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya na 2023.

Ku tuna cewa tsohon shugaban ƙasar ya goyi bayan Obi ne a matsayin ɗan takarar da ya fi so gabanin zaɓen Shugaban Ƙasa.

Jim kaɗan bayan ƙidaya sahihan ƙuri’u a mazaɓar Obasanjo da ke gunduma 11, Unit 22, a Ƙaramar Hukumar Abeokuta ta Arewa a Jihar Ogun, ɗan takarar Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu, da ƙuri’u 56 ya kayar da Obi.

Idan aka yi la’akari da yadda aka yi zaɓen, Obi ya samu ƙuri’u 9, sannan ɗan takarar Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya samu 7, yayin da Tinubu ya samu ƙuri’u 56 a matsayin mafi yawan ƙuri’u.

Ƙuri’un da ba su da tushe a rumfar zaɓen sun fi na Atiku da Obi na ɗaiɗaikun ƙuri’u, yayin da ƙuri’u 10 suka lalace.