Dattawan Ibo a Aso Rock

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Gaskiya ne kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi kama daga kan jemage, bilbili, kuruciya, hasbiya, farar daka zuwa kanari mai daɗin kuka da sauransu. Ma’ana labarin zuciya a tambayi fuska. Duk abun da ka ga mutum yana yi to akwai wani abu a ransa ko in ce zuciyarsa ta kan raya masa yin hakan ta hanyar alheri ne ko akasin hakan.

Gabanin 1914 Nijeriya na rabe gida biyu shiyyar Arewa da Kudu. A wancan tsohon zamanin Turawan mulkin mallaka sun yi wa yankin Arewa mulki a kaikaice ta hanyar bi ta hannun sarakuna don samun yankin da tsarin shugabanci, addini da al’adu irin na jama’ar yankin har ma da ilimin rubutu da karatu. A kudu kuma Turawan na mallaka da su ka faro shigowa Afurka a ƙarni na 16 sun yi wa yankin mulki ne na kai tsaye don hakan ne ya dace da mutanen da ke zaune a yankin.

Duk da Yarbawa sun yi dauloli irin na su amma ba daular da za a ce in ta yi magana duk sauran birane da ƙauyukan Yarabawa za su amince. In aka shiga yankin Kudu-maso-gabar inda Igbo su ke rayuwa, ba tasirin sarauta ko ma wani dattijo da ake jin maganarsa. Daga bisani ma mafi darajar mutum a yankin shi ne mai hannu da shuni ko wanda ya samo kuɗi ta kowane irin hali. Hakan ya ba wa Turawa sauƙin cusa addini da al’adun a tsakanin mutanen Ibo. Ta kai ma Ibo ya fi ganin Bature da cewa, shi ne mafi darajar jinsi a duniya. Da tafiya ta yi tafiya sai wasu Ibo su ka riƙa yayata cewa asalinsu daga ƙasar Yahudun Isra’ila suka fito, don haka su na jin alfahari in ka alaƙanta su da Yahudawa.

Idan za a tuna lokacin da shugaban ƙungiyar ‘yan awaren IPOB Nnamdi Kanu ya arce daga belin da Jostis Binta Nyako ta babbar kotun tarayya ta ba shi, can Isra’ila ya nufa ya na mai sanya sutura irin ta limaman addinin YAHUDU. Mabiyan sa a Nijeriya na jin daɗi da jinjina ma sa cewa ya samu mafaka a ƙasar kakannin su. Da wannan shimfuɗa zan tsunduma kan darashin ALƘIBILIYAR wannan mako da ta shafi ziyarar da dattawan ƙabilar Ibo su kai fadar Aso Rock.

Ƙarin bayani a kan dattawa, wannan ajin mutane ne da son samu masu yawan shekaru fiye da 60-75 har ƙarshen rayuwa da kan ba su wata kima ko banza ta daɗewarsu a duniya da kan ba su ilimin sanin abun da ya faru a jiya da shekaranjiya. Duk da haka akwai wata zolaya a arewa da kan fassara dattijon da ba shi da dattaku wato ɗabi’u masu nagarta da cewa, “dattijon Wukari ne”. Ko yaya dattawan Wukari a jihar Taraba su ke?, zan tsaya a nan da fatar zolaya ce kawai don ba mamaki a samu dattijo a Wukari mai mutunta al’adarsa da addininsa.

Dattijon ƙabilar Ibo mai shekaru 93 Chief Mbazulike Amarchi ya jagoranci tawaga ta wasu dattawan ƙabilar Ibo zuwa fadar Aso Rock inda ya buƙaci shugaba Buhari ya ba shi shugaban ‘yan awaren Biyafara IPOB Nnamdi Kanu ya tafi da shi don zai iya hana shi surutan da ya ke yi; wato ma’ana zai iya gyara ma sa ɗabi’a daga mai baƙaƙen maganganu kan dunƙulalliyar Nijeriya zuwa mai faɗar alheri ko ma dai aƙalla ya yi shiru ko da kenan ba ya qaunar cigaba da zama a matsayin ɗan Nijeriya.

Cif Mbazulike Amaechi wanda ya na daga cikin ‘yan majalisar dokoki a jamhuriya ta farko kuma tsohon ministan sufurin jiragen sama ne, ya ce, ana matuƙar girmamashi a ƙasar Ibo kuma ba ya son barin baya da kura in ya bar duniya. Amaechi ya nuna a halin da a ke ciki yankin na cikin ruɗani da samun koma bayan tattalin arziki.

Labarin dai bai nuna ko dattijon ya aza sashen alhakin kan umurnin da IPOB ke bayarwa a ranakun litinin na tilastawa mutane su zauna a gida. Don haka ba buɗe kasuwanni ko hada-hadar yau da kullum. Wanda ya yi garajen fitowa, ya na kasadar rasa ransa. Haka kawai ma ‘yan awaren sun sha buɗe wuta kan ‘yan arewa da kan buɗe tukubar tsire da dare ko wasu harkokin neman kuɗi da kan gudana in duhun dare ya shigo.

Baya ga haka an haƙƙaƙe cewa, ‘yan awaren ne su ka buɗe wuta kan tsohon mai ba wa shugaba Jonathan shawara kan siyasa Alhaji Ahmed Ali Gulak a garin Owerri na jihar Imo lokacin da ya ke ƙoƙarin tafiya filin jirgi don dawowa Abuja.

Amaechi ya ce, yanzu haka kasuwanci da sauran lamura sun rikice a ƙasar Ibo; ya na mai buƙatar shugaba Buhari ya zama wanda za a tuna shi a matsayin mai kashe wutar fitina in ta kama. Kashe wutar a bisa manufar wannan ziyara shi ne sake Nnamdi Kanu ya koma gida ala bashi za a samu sararawar lamura kamar yadda Chief Amaechi ya ke nunawa kuma ya na tunanin hakan zai ɗore ko bayan ransa.

Nan take mutane musamman daga arewa su ka fara tambayar me ya sa duk ta’asar da Nnamdi Kanu ya yi da zuga jama’ar Ibo ta shirin rediyonsa na Biyafara ba su hana su ba?, in kuma sun hana su me ya sa ba su hanu ba?, hakan ya nuna ‘yan IPOB ba sa mutunta manyan ‘yan ƙabilar ta su kenan kuma ba mamaki su ma manyan kafin wannan lokacin ba sa sha’awar tsawatawa matasan don ta kan iya yiwuwa ma su na mara baya ga abun da ‘yan bindigar IPOB ke aikatawa na farautar wanda ba Ibo ba su harbe ko kuma su kama ƙalilan daga Igbo da ba sa cikinsu, su ci mu su zarafi ko ma su hallaka su.

Shugaba Buhari ya ce, wannan lamari ya na hannun kotu, kuma ba wanda zai shaide shi da tsoma baki a lamuran kotu. Duk da haka shugaban ya ce, zai duba buƙatar tsohon.

A na tuhumar Kanu da laifin cin amanar ƙasa da ta’addanci a shari’ar da za a cigaba da yi ma sa a ranar 19 ga watan Janairu 2022.

A babin adalci shi ne a bar shari’a ta yi aikin ta. Gwamnatin Nijeriya ta cigaba da gabatar da hujjoji gaban kotu na tuhumar Kanu da waɗannan miyagun laifuka. Su kuma lauyoyin Kanu su kaucewa biris da darajar kotu da hakan har ya kai su ga ficewa gabanin shigowar Jostis Binta Nyako don wai jami’an DSS sun hana wani lauya da ya zo takanas daga Amurka don kare Kanu.

Da dai da gaske duk Ibo na son samun ƙasar Biyafara, sai su miƙa buƙata ta hanyar wakilansu a majalisar dokokin tarayya su gabatar a yi muhawara don bin tsarin mulki wajen duba kadun wannan muradi.