Buhari ya ce zai fara bai wa ’yan Nijeriya kuɗin mota idan ya cire tallafin mai

Daga BASHIR ISAH

’Yan Nijeriya kimanin kimanin miliyan 40 ne za su riƙa samun Naira 5,000 duk wata a matsayin kuɗin mota daga aljihun Gwamnatin Tarayya, don rage raɗaɗin cire tallafin mai bakiɗaya ya zuwa baɗi idan Allah Ya kai mu.

Gwamnati ta bayyana haka ne ta bakin Ministar Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed, a wajen ƙaddamar da shirin Bankin Duniya na ‘Nigeria Development Update’ (NDU) a ranar Talata.

Idan dai za a iya tunawa, a baya gwamnati ta bayyana cewa, ya zuwa watan Yuli na 2022, za ta cire tallafin mai bakiɗaya.

Gwamnatin ta ce adadin waɗanda za su ci gajiyar wannan shiri ya dogara ne da abin da ya rage wa gwamnati a cikin asusunta bayan ta kammala janye tallafin man bakiɗaya, inji ministar.

A cewarta, “kafin lokacin da za a janye tallafin man bakiɗaya a tsakiyar 2022 muna aiki tare da abokan hulɗarmu wajen samar da tsare-tsaren da za su taimaka wajen rage raɗaɗin in cire tallafin ga talakawa wanda yawansu ya kai kashi 40 cikin 100 na yawan ‘yan ƙasa.

“Ɗaya daga cikin waɗannan tsare-tsaren shi ne bada tallafin kuɗin mota na Naira 5,000 duk wata ta tsarin ‘cash transfer’ ga ‘yan Nijeriya da suka cancanta su miliyan 30 zuwa 40.

“Muna da yaƙinin cewa ci gaban da aka samu a fannin fetur a baya-bayan nan, kamar samar da Dokar Masana’antar Fetur (PIA) 2021, da kuma sake farfaɗo da matatun mai na gwamnati guda 4 da ake da su a ƙasa, haɗi da samuwar wasu matatun mai masu zaman kansu a 2022, hakan zai bada gudunmawa mai gwaɓi ga ƙoƙarin bunƙasa tattalin arzikinmu.”

Bayanin Bankin Duniya ya nuna cewa kashi 40 na talakawan Nijeriya na amfani da ƙasa da kashi 3 ne kacal na man da ƙasar ke samu. Tare da haskaka cewa, attajiran ƙasar su ne suka fi cin moriyar tallafin.