Dawo da tallafin man fetur zai sa talauci ya tsananta a Nijeriya, inji Daraktan NOA

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Darakta Janar na hukumar Haɗin-kan Ƙasa, NOA, Issa-Onilu ya yi kira ga ƴan Nijeriya da su tsara hanyoyin gudanar da rayuwa a yanayin matsin tattali da ake fama da shi a sakamakon cire tallafin man fetur a ƙasar da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi.

A wata hira da gidan talabijin na ‘channels’, Issa-Onilu wanda tsohon mai magana da yawun jam’iyyar APC ne, ya ce talauci zai yi tsanani matuƙar aka dawo da tallafin mai kamar yadda masu zanga-zangar tsadar rayuwa su ka buƙaci a yi a makon da ya gabata.

Ya ce, duk mai neman a dawo da tallafin, maslaha ce ta kai-da-kai gare shi ba ta tattali ba, ya na mai cewa sai an tabbatar da cewa hakan zai warware matsalolin talauci kafin a nemi mayar da shi.

Ya kuma da shawarci al’umma cewa su nemi hanyoyin gudanar da rayuwa a halin cire tallafin man fetur.

Ya kuma bayyana irin alaƙar da ke tsakanin talakawa da ƴan siyasa na yin alkawari a saɓa a lokuta da dama a ƙasar.

A ranar Lahadi ne shugaba Tinubu ya yi watsi da batun dawo da tallafin man fetur a Nijeriya.

Kazalika, janye tallafin man fetur ya sanya farashin lita ya yi tashin gwaoron zabi inda daga wajen N200 ya kai har zuwa sama da N700 wanda hakan ya sa farashin ababe da dama ya tsananta a Nijeriya.

By Babaji