Yanzu-yanzu: Shugabannin tsaro na ECOWAS na ganawa a Abuja

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Shugabannin tsaro na ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka, ECOWAS na ganawa a helkwatarta tsaro da ke Abuja.

Shugaban Hukumar Ma’aikatan Tsaro ta Nijeriya, Janar Christopher Musa wanda shi ne kuma shugaban kwamitin shugabannin tsaro na ECOWAS shi ke jagorantar zaman.

Mahlarta taron sun haɗa da; Ministan Tsaro, Muhammed Badaru, Ministan harkokin ƙasashen waje, Yusuf Tuggar da kuma shugaban kwamitin Majalisar Dattijai kan harkokin tsaro, Ahmed Lawan.

Sauran sune; shugaban kwamitin Majalisa kan tsaro, wakilin Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro, shugabannin ma’aikatu, shugabannin hukumomin tsaro na ƙasashe face na Mali, Burkina Faso da Nijar.

By Babaji