Me ya sa matasa ke wa malamai rashin kunya?

Spread the love

Daga Imam Hassan Imran

Assalamu Alaikum. ‘Yan’uwana, yau na zo da wata taƙaitacciyar nasiha ne ga ‘yan’uwa matasa da malamai, da nufin ba da shawarwari da samar mafita.

Abu ne da muka sani, malamai a matsayin su na Magada Annabawa su ne Allah ya ɗora wa nauyin ilamantar da al’umma da kuma tabbatar cewa sun kafu akan hanya maidaidaiciya. Malamai suna taka rawar gani wajen inganta tarbiyyar matasa da ta sauran al’umma.

Amma abin takaici kuma abin haushi shi ne yadda matasa suke nuna rashin kunya ga malamai a wannan zamani. A ‘yan makwannin da suka gabata, malamai daga ɓangarori daban-daban sun yi ta bayanai da jan hankulan matasa akan illar zanga – zanga, wanda wasu matasa suka yi kunnen shegu da kiraye-kirayen da malaman suka riƙa yi musu. Wasu a cikinsu har zagi da cin mutuncin waɗannan malamai masu martaba suka riƙa yi a shafukan sada zumunta.

A ganina, daga cikin abubuwan da suka janyo wannan rashin kunya da matasa suka riƙa yi wa malamai shi ne, sukar da malamai suke wa junansu akan aƙida ko bambancin fahimta, a kan minbari da kuma wuraren darasussuka na addini a masallatai. A yayin da irin waɗannan malamai suke sukan junansu, mabiyansu wanda mafi yawansu matasa ne sai ka ji sun kama ihu suna ta kabbarori suna faɗin ‘Allahu Akbar.’ Hakan kuma na ƙara zuga malaman da kambama musu kai. Suna mantawa da karin maganar nan da ke cewa, kaza ta daina murna don ta ga ana jan hanjin ‘yar’uwarta, wataƙila ita ma za a ja na ta ba da daɗewa ba. Tabbas, babu mamaki ire-iren waɗannan matasa masu rashin kunya suna koyo wannan hali ne daga irin malaman da suke ɗaukar karatu da darasu a wajensu ne.

Daga cikin abubuwan da ke ƙara rura wutar rashin kunya ga matasa shi ne shafukan sada zumunta. Yanzu, harkar sadarwa da yaɗa saƙonni ta zo mana da sauƙi sosai, an samu cigaba da canje-canje, musamman ta manhajojin Facebook da Whatsapp waɗanda mutanen mu suka fi mu’amala da su. Wannan na daga cikin dalilan da ya sa matasa suke amfani da su yadda suka ga dama. A wasu kwanakin da suka shuɗe kafin zanga–zangar ranar Alhamis ta makon da ya gabata, matasa sun yi ta sukan junansu har da malamai musamman waɗanda ra’ayinsu suka saɓa da na su.

A ranar na buɗe wayata ina duba saƙonni a Facebook sai na ci karo da wani saƙon bidiyo da abokina ya ɗora na ɗaya daga malaman mu wanda yake suka kan zanga–zangar da ake shirin yi a lokacin ta mahangar addini. Sai na lura da sashin tofa albarkanci baki na mabiya, abin da na gani ya yi matuƙar ɗaga min hankali, don yadda na ga matasa suna ta zagin malamin tare ta ci masa mutunci da sauran kalamai na ɓatanci akan shi. Raina ya ɓaci sosai, nasan cewa wannan lalacewar tarbiyya ta kai bango, kuma idan ba a ɗauki hanyar gyara ba al’ummar mu da jikokin mu sun shiga uku.

Tabbas, masu iya magana na cewa idan ɓera na da sata to, daddawa ma tana da wari. Wasu malaman su ne suke janyo wa kansu zagi da rashin kunyar matasa. Wasu malaman basu kama girmansu kuma basu kula da kalmomin da ya kamata suna amfani da su a wuraren wa’azozinsu. Wasu malaman kuwa son abin duniya ya toshe masu baki basu iya furta gaskiya. Ta yaya matasa za su ɗauke su da daraja?

Daga cikin hanyar mafita da za mu magance wannan rashin kunya ta matasa ga malamai shi ne, malamai su ji tsoron Allah su karantar da al’umma gaskiya, su kuma bada kyakyawar kulawa ga tarbiyyar matasa a dukkan wa’azozinsu. Malamai su gujewa sukar junansu a harkokin addini ko ta rayuwa, musamman a inda ra’ayinsu ya sha bamban. Idan malamin ƙungiyar Izala ya mutunta ya kuma darajanta malamin Ɗariƙa, mabiyansu su ma za su bi tafarkinsu.

Hakanan kuma, matasa su yi amfani da shafukan sada zumunta a hanyoyin da suka dace. Mu sani cewa akwai ranar hisabi da kowa zai tsaya a gaban Allah ya yi masa bayanin abinda ya wallafa a shafinsa. An san mu ‘yan Arewa da tarbiyya da kuma mutunta na gaba da mu musamman malamai, mu koma kan wannan tafarkin da iyayenmu da kakaninmu suka tarbiyyartar da mu akai.

A ƙarshe, malamai su nemi sana’ar dogaro da kai, su gujewa zama suna jiran abin da wani zai basu, suna bara da tumasanci. Malamai su yi riƙo da kyawawan halayen magabata, kamar irin su tsoron Allah, faɗan gaskiya, adalci, haƙuri da kula da haƙƙoƙin al’umma da sauransu.

Allah Ya kawo mana sauƙin rayuwa ya kuma shirya mana matasanmu. Amin

  • Imam Hassan Imran ya aiko da wannan nasiha ne daga Jos, kuma za a iya samunsa kan lambar waya 0905 932 3221.
By ukarofi