Hukumar DSS ta kama ƴan ƙasar Poland bakwai a Kano bisa hannu a zanga-zanga

Spread the love

Aƙalla ƴan ƙasar Poland bakwai hukumar ƴan sandar farin kaya na DSS ta kama bisa zargin hannu a cikin zanga-zangar yunwa da ke gudana.

Wakilin DSS ne ya bayyana haka a yayin wata ganawa da ministan harkokin ƙasar waje Yusuf Tuggar.

Wakilin yayin zantawa da manema labarai ya bayyana cewa an cafke su ne da bayyana tutocin wasu ƙasashe a yankin Arewa maso Yamma.

Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da ministan ƴaɗa labarai, Sufeton janar na ƴan sanda da ciyaman kwamitin majalisa harkokin ƙasashen waje.

By ukarofi