Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
(Ci gaba daga makon jiya)
MANHAJA: Yaya alaƙarki take da masu bibiyar littattafanki, kuma ta yaya ki ke hulɗa da su?
MUM AMNASH: Haƙiƙa akwai ingantacciyar alaƙa tsakanina da ma’abota bibiyar rubuce-rubucena. Duk da na kwana biyu ba na rubuta dogwayen labarai, har yanzu mukan gaisa da wasu. Wasu kuma sukan kira don bibiyar ƙarashen labaran da ban ƙarasa musu ba. Tsakanina da su sai fatan alkairi.
Yaya ki ke samun jigo ko basirar yin rubutunki?
Ina samun jigo ta hanya mai sauƙi, daga abubuwan da suke zagaye da ni. Kusan duk labaraina, jigon zamantakewa ne kan abubuwan da suke faruwa yau da gobe, masu daɗi ko kuma akasin haka. Jimla ɗaya idan na ji, za ta iya samar da faffaɗan tunanin da zan iya bin bayansa da bincike sannan na dasa fandishan gina labari; har na miƙa saƙon da nake son isarwa ga al’umma. Misali: Kwanakin baya ina tafiya a kan titin Gwarzo zan tafi makaranta, sai na ga wani mai motar tifa ya lodo yashi, amma bai rufe yashin da leda ko wani abu ba. Wanda kai tsaye idan iska ta ɗebi wannan yashin zuwa idanun sauran masu tuƙa ababen hawa musamman babura, za a iya samun afkuwar haɗari. A kan wannan abin da na gani, na rubuta gajeren labari.
Kina daga cikin gwarazan Gasar Hikayata ta BBC Hausa na 2022, gaya mana sirrin samun nasarar ki, kuma sau nawa ki ka shiga gasar?
Na shiga gasar Hikatata ta BBC Hausa sau biyu. A shekarar 2021 labarina bai fito ba. Da wata shekarar ta zagayo, cikin ikon Allah sai sunan labarina ya fito a zagayen farko. Na yi mamaki matuƙa gaya, don da Nana Aicha ta turo mini da jerin sunayen labaran, kasa ganin sunan nawa na yi. Sai da ta nuna mini, sannan na ga shi ne na uku a jerin. Sirrin samun nasarata a gasar Hikayata, bai wuce addu’a ba, don a lokacin kwata-kwata ban taɓa hasaso nasara ba. Na ma fi hanƙoro da burin na samu tsallakawa zuwa matakin farko, don na rabauta da shaidar karramawa. Sai dai, bayan na rubuta labarin da zan shiga gasar da shi a 2022, na ba wa Malama Nana Aicha Hamissou ta duba mini, saɓanin na baya da ni kaɗai na yi kiɗana na yi rawata. Kuma ita ta ƙarfafa min gwiwa, amma har na sare na fara tunanin rubuta sabon labarin da zan shiga da shi. Duk da bai kwanta min ba, haka na tura shi a ƙasa da awa ashirin da huɗu a rufe gasar; na bi bayansa da addu’a. A nan ɗaukar shawarar na gaba, ta yi min amfani matuƙa gaya. Da yake da rabo sai ga shi labarin ‘Al’ummata’ ya zo mataki na uku.
Wanne canji wannan nasara ta kawo a rayuwarki?
Haƙiƙa nasara a gasar Hikayata ta kawo canji a rayuwata daga fuskar da ba a sani ba, zuwa wadda aka gane. Duk yadda nake baya-baya da mutane, wannan nasara ta sa na buɗe hannayena, na kuma yi maraba da ɗaukacin waɗanda suka taya ni murna waɗanda na sani da ma waɗanda ban sani ba. Ta kuma rage mini kaso mai yawa na tsoron da nake da shi matuƙa gaya, wanda idan a baya ne, tsayuwa a gaban mutane ko da ba zan furta komai ba, ba ƙaramin lamari ba ne a gare ni.
Ban da Gasar Hikayata, kin taɓa samun nasara a wasu gasanni da ake shiryawa na marubuta? Kawo sunan gasar, shekarar, da sunan labarin da ki ka shiga gasar da shi.
E, na samu nasara a wasu gasannin ban da Hikayata, a wasu kuma labaraina sun tsaya a matakin farko ne, ba su tsallaka zagaye na gaba ba.
Akwai gasar ƙungiyar Jarumai Writers’ Association ta shekarar 2022, na sami nasarar zuwa ta uku da labarina mai taken ‘Mugun Gani’. Sannan a cikin wannan shekarar harwayau na samu nasara a gasar zauren Marubuta Group na WhatsApp, inda labarina mai taken ‘Takwara’, ya zo na ɗaya. Na shiga wannan gasa aƙalla sau tara zuwa goma, kafin na samu nasara a 2022. Tun da na fara shiga, babu watan da na tsallake ban shiga ba, sai dai idan ba a yi ba. Wannan gasa ta taimaka mini ƙwarai da aniya, har na ɗan fara gane yadda ake gina gajeren labari. Dayake ana fitar da makin jigo, balaga da kuma ƙa’idojin rubutu, wannan ya sa na gane inda nake da rauni sosai, sannan na fara laluben mafita. Haka ma a shekarar 2024 na sake samun nasara a gasar zaauren Marubuta Group, wacce na shiga da labarina mai taken ‘Rigar Aro’ inda labarina ya zo mataki na shida, kuma labarin yana cikin littafin ‘Abin Cikin ƙwai’ da aka wallafa.
A wannan shekara ta 2024 na shiga gasar zauren Aji Na Musamman na WhatsApp, inda shiga da rubutacciyar waƙa mai taken ‘Ummu Amra’ (Gasa ce da Malam Jibrin Adamu Rano ya saka, tare da bada zaɓin a yi rubutun zube ko rubutacciyar waƙa, sai na zaɓi waƙa.) Sannan kuma na shiga gasar zauren Marubuta Group, da wata rubutacciyar waƙa mai taken ‘Muhimmancin Haɗin Kai’ inda kuma Allah ya bani nasara na zama ta ɗaya.
Wanne abu ne za ki iya cewa ya kawo sauyi a rayuwarki ta dalilin rubutu?
Rubutu ya kawo min sauyi sosai wurin tilasta min yarda da rukunin wasu mutanen da ba ahalina, ƙawayena ko abokan karatuna ba.
Ba ni da saurin sabo kwata-kwata, ba kuma na sakewa da duk wanda bai cikin mutanen da na ambata. Amma zuwa yau, sakamakon kyakkyawar mu’amala da yadda marubuta ke ja na a jiki, ta kai ta kawo marubuta sun zama wasu dangina da jini ne kawai bai tsarga a tsakaninmu ba. Ban taɓa ganin rukunin mutane kamar marubuta ba, suna da sadaukarwa, ƙaunar juna da kuma haɗin kai. A marubuta ne, mutum zai shiga gasa, amma sai ya manta da kansa ya yi iyakar bakin ƙoƙarinsa wurin taimakawa marubuci ɗan’uwansa ta hanyar tsifa da taje rubutunsa. A ƙarshe kuma duk wanda ya samu nasara a haɗu a yi farinciki da murna tare. Rubutu ya yi mini riga ya yi min zani, na iya cewa har da fatala da mayafi. Dalili kuwa, a sanadiyyar zama da marubuta na samu ilimin da ban samu a makaranta ba. Ban gane haka ba, sai da ya zamo ɗan abin da na sani dangane da ƙa’idojin rubutu na daɗa cicciɓa darajar makina a kowanne zangon karatu. A zangon aji uku na biyu, da ya gabata, na ɗauki wani kwas mai taken ‘Hausa Fictional Prose (Hau 3310)’ wanda Dr, Halima Abdulƙadir ɗangambo ta ɗauke mu, ni kaɗai ce mace, sai maza goma sha shida, amma ban sare ba. Rubutu da marubuta sun sauya rayuwata daga mara ƙwarin gwiwa, zuwa mai yunƙurawa da son fafutukar cimma burinta a zahiri ba a baɗini kaɗai ba; don a dama da ni a abubuwa da dama. Madallah da wannan sauyi.
Yi mana ƙarin haske kan littafinki na ‘Rai Da Motsi’, kuma me ya ja hankalinki ki ka rubuta shi?
‘Rai Da Motsi’ labari ne da na shiga gasar Gusau Institute 2022 da shi, bai kuma tsallaka mataki na gaba ba, kamar yadda na bayyana a baya.
Jigon labarin ya haɗa abubuwa daban-daban, waɗanda kai tsaye sun shafi matsalolin da masu buƙata ta musamman ke fuskanta, da kuma yadda idan suka saka yaƙini suka motsa za su kai ga ci, ba tare da nakasarsu ta yi musu shamaki ba. Duk da tauraruwar littafin hannu ta rasa, dalili ya yi dalilin da na sako nakasa ta baɗini don haska wa Mas’uda hanya bayan baƙin duƙununin duhu na neman dafar da rayuwarta. Bayan haka, ta yi iyakar bakin ƙoƙarinta wurin taimaka wa jaririyar da ke ɗauke da lalurar nakasar ƙwaƙwalwa ta Down Syndrome, wadda wasu suke kira da ‘Galhanga’.
Samun wannan gaɓar, ya sa na yi bincike dangane cutar da abin da na sani a kan cutar, saboda muna da yarinya mai wannan lalurar wadda ta kasance ta biyu a gare mu. Marubuciya Dr. Hamisha, ita ta fara yi mini bayanin larurar a ilimance bayan ɗan abin da na sani a lokacin da muka yi zaryar asibiti. Daga baya Hajara Ahmad (Oum Nass) ta taimaka mini wurin tartara wasu bayanan. Na rubuta tambayoyin da nake da su, ta ba wa Dr, Ishaƙ Birniwa ya amsa mini. Sai kuma ma’aikatan jinya, Aisha Muhammad Auwal, Ummi Garkuwa da Amina Shu’aibu Yakub sun taimaka min su ma. Bayan nan, na duba Google sosai, hasali bayanan da na tartara ba duka suka shiga cikin Rai Da Motsi ba. Wannan ya sa na ƙara ɗaura aniyar gina wani labarin a kan Down Syndrome ɗin, wanda shi ma na yi nisa sosai a rubutun, don wannan matsalar ni ma ina cikinta, tun da abin da ya taɓa ido ya shafi hanci. Zan kuma yi iyakar iyawata wurin wayarwa da al’umma kai don su gane ba matsalar aljanu ba ce ko mayu. Larura ce da kafatanin masu ita duk inda suke a faɗin duniya, suna da siffofi guda, kuma gadonta ake yi.
A cikin Rai ‘Da Motsi’, na haska wasu matsalolin da suka shafi ilimi da kuma muhimmancin bunƙasawa da zamanantar da ƙananun sana’o’i. Da sauran batutuwa da dama.
Menene burinki nan gaba a matsayinki ta marubuciya?
Ba ni da burin da ya wuce na tura saƙon da zai inganta rayuwar al’umma, ko da kuwa a ce mutum ɗaya ne zai amfana rayuwarsa ta sauya. Zan yi farinciki matuƙa, har na bugi ƙirjin cewar ni marubuciya ce; tun da buƙatar ma je Hajji sallah. Sannan ina da burin rubuta littattafan wasan kwaikwayo, waɗanda tun da aka fari, labaran zube da waƙa suka yi musu fintinkau. Zan so a ce watarana idan da rai da lafiya, da yardar Allah na zamo daga cikin waɗanda zakaransu zai yi cara a wannan ɓangare.
Wanne abu ne ya fi damunki a harkar rubutu da ki ke so in kin samu dama ki kawo gyara?
Babbar matsalar da ta fi ci mana tuwo a ƙwarya ba ta wuce ta marubutan batsa ba, waɗanda kan lafe a ƙarƙashin ‘Adabin Bariki’ suna cin karensu babu babbaka. Abin takaicin da yake wake ɗaya ke ɓata gari, sun bi sun yaɓe mu da kashin kaji ana yi mana kuɗin goro mu marubutan yanar gizo. Duk da a yanzu matsalar ta ɗan ragu ba kamar baya ba. Kasancewar adabi madubin da ke haska rayuwar al’umma, babu ta yadda za a yi a hana marubuci yin rubutu a kan wani abu da yake faruwa a rayuwar al’umma, sai dai wuce makaɗi da rawa bai zama lallai ya haifar da ɗa mai ido ba, kamar yadda marubutan batsa ke tashi a tutar babu. Babban abin da zan yi idan na samu dama, bai wuce nuna musu bambancin rubutu a kan bariki da kuma tantagaryar batsa ba. Ba zai yiwu a ce za a yi rubutu a kan bariki ba, a kuma sanyawa ma’abotanta kalamai da ɗabi’u irin na salihai ko malamai ba. Bal, idan aka yi hakan zai zama kufcewar salo. Kowanne rukunin masu sana’a ko wani aiki akwai kalmomin da suke keɓaɓɓu a gare su, wanda idan mutum ba ya ciki bai zama lallai ya fahimci inda aka dosa ba. Me zai hana marubuci ko marubuciya su yi bincike su gano waɗannan kalmomin, kuma su yi amfani da su?
A lokacin da ake haya da motocin bas, idan kwandasta ya ga direba zai tsaya a ɗauki wasu fasinjojin, yana iya ce masa, ‘Ja mu je Oga, jarkoki ne.’ Kalmar jarka tana nufin na gida ne, idan an ɗauke su ba kuɗi za su biya ba. Amma har a yi a gama, bai zama lallai mutum ya gane inda suka dosa ba. Duk da ni almajira ce da ba ta wuce matakin ƙolanta ba, a iyakar karatun da na yi na Fiƙhu a gaban malamaina, suna saye kalmomi da dama su fassara mana da wadda za ta yi daidai da tunani da hankalinmu. Akwai kalmomin da suka zo a cikin littafin ‘ƙawa’idi’ ba a fasa su ba, sai a cikin ‘Izziyya’. A cikin Alƙur’ani mai girma, Allah maɗaukakin Sarki ya kira mata da gonaki, shin wannan ba sayawa aka yi ba?
Duk da an hana ihu ba a hana aha ba, su yi rubutunsu a kan bariki, amma dai a sakaya duk wata kalma da ba za ta faɗu a gaban iyaye, ƙanne da ‘ya’ya ba, don kunya da imani abokan tagwaitar juna ne.
Idan kuwa har jan hankali, ban baki da rarrashi bai yi amfani wurin sauya akalar rubutunsu ba to, ba zai zama da laifi don an tursasa su ta hanyar amfani da doka ba, tun da duka a ƙarƙashinta muke.
Kina ganin akwai wata rawa da gwamnati za ta iya takawa don kawo cigaba a harkar rubutun adabi?
Akwai rawar da gwamnati za ta taka wurin inganta rubutu, har ya amfanar da ita, marubuta da ma al’umma bakiɗaya. A baya, tatsuniya ita ce makarantar ‘ya’yan Bahaushe ta farko wadda a cikinta ake tura saƙo ga yara da umartar su da kyawawan ayyuka da hani ga munana.
Misali: A cikin littafin Tatsuniyoyi Da Wasanni na Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya, (Allah Ya gafarta masa) akwai tatsuniyar ‘Na Goma’, wannan tatsuniya tana nuna illar sata ƙarara ko da kuwa kayan mahaifa ne. A ƙarshenta kuma, an nuna muhimmancin yafiya, bayan iyayen Nagoma sun karɓo shi daga hannun Dodanniya.
A wani taro da na halarta a watannin baya, an yi ƙorafin a kan yadda ɗabi’ar karatu ke neman yin ƙaura a tsakanin yara da matasa. A ƙarshe aka tono cewa, matsalar rashin wadatattun littattafai ita ta zamo kanwa uwar gami wurin ƙara wa wutar fetur. Domin kawar da wannan matsala, akwai marubuta masu tarin hikima da basira da za su samar da waɗannan labara. Gwamnati za ta iya bunƙasa harkar rubuce-rubuce ta hanyar ƙara samar da hukumomin talifi.
Gwamnati za ta iya ɗaukar nauyin rubuce-rubuce don bunƙasa adabi, ta kuma yi amfani da wannan dama ta tura saƙon da zai amfanar da al’umma. Misali: Yaƙi da cin hanci da rashawa, kishin kai, kishin ƙasa, tsafta, muhimmancin noma da sauran muhimman abubuwa. Idan kuma an rubuta, ta sahale karanta su a makarantu da gidajen rediyo, don ya kasance haƙa ta kai ga cimma ruwa.
Wanne abu ne ya fi faranta miki rai a mu’amalarki da marubuta?
Haɗin kai, zumunci, ƙaunar juna da kuma yadda suke tsayuwar tsayin daka ga junansu a yayin dariya ko kukan ɗaya daga cikinsu. Wannan yana faranta mini rai.
Wanne abu ne ya fi sa miki nishaɗi a rayuwarki?
Abubuwan da ke saka ni nishaɗi a rayuwata suna da yawa. Na wayi gari cikin Musulunci da rai da lafiya, tare da ahalina yana saka ni farinciki.
Haka kuma a duk lokacin da aka kafe mana sakamakon jarrabawa na ga darajar makina ta ɗaga, nakan yi farin ciki matuƙa gaya. Ba don kaina kaɗai ba, don zan wanzar da farinciki ga jigon da ya yi tsayuwar tsayin daka wurin ganin na cika burina a ɓangaren neman ilimi. Rashin ba shi kunya, la’akari da sadaukarwarsa gare ni, yana sani farinciki sosai. A wasu lokutan zan fita da sassafe, ba kuma zan dawo gida ba sai almuru. Amma duk wata kafa da za ta zamo cikas gare ni, wanda nake tare da shi yana iyakar ƙoƙarinsa wurin liƙe ta. Haka kuma a duk lokacin da na wanzu a cikin dangina, ina samun farinciki mai tarin yawa; musamman kakata, yayye da ƙannen mahaifiyata. Sai kuma samun cigaba a sana’ata, wannan ma yana saka ni farinciki.
Kin taɓa yin rubutun fim ko kina da sha’awar rubutawa nan gaba?
Ban taɓa rubuta film ba, na dai taɓa halartar wani aji a yanar gizo na koyon yadda ake rubuta shi. Idan dama ta samu, in sha Allahu zan yi.
Wacce karin magana ce ke tasiri a rayuwarki?
Sannu ba ta hana zuwa, sai dai a daɗe ba a je ba.
Masha Allah. Muna godiya.
Ni ce da godiya.
