Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Ƙungiyar Kare Haƙƙin Musulmi (MURIC) ta yi kira ga hukumomin tsaro su gargadi Datti Baba-Ahmed, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar LP kan cewa kada CJN ya rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Farfesa Ishaq Akintola, Babban Direktan MURIC, ya ce akwai ganganci cikin kalaman na Baba-Ahmed.
Baba Ahmed ya buƙaci Olukayode Ariwoola, babban alƙalin alƙalan Nijeriya, kada ya rantsar da zavavcen shugaban qasa Bola Tinubu, yana mai cewa hakan saɓa Kundin Tsarin Mulkin ƙasa ne.
Ya yi wannan furucin ne yayin da ya ke tsokaci kan gaza samun ƙuri’u kashi 25 na birnin tarayya Abuja a zaɓen shugaban ƙasa na watan Fabrairu.
Fasarar sashin doka da ya yi magana kan hakan na cikin abubuwan da za a tafka muhawara a kansa a kotun zaɓe.
“Kalaman Datti tamkar kira ne ga sojoji su yi juyin mulki”, in ji Farfesa Akintola.
Akintola ya ce, kalaman Baba-Ahmed kan batun daidai ya ke da cewa a yi juyin mulkin soja.
Ya yi kira ga shugabannin addini da waɗanda abin ya shafa su ja kunnensa’ kan furta maganganu da ka iya tada zaune tsaye.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ya ce, “Hakan na nufin tada kayan baya da neman juyin mulkin soja. Babu wanda ya yi imani da dimokraɗiyya da zai furta hakan. Idan jami’an tsaro ba su gargaɗe shi da irinsa ba, ba su cika aikinsu.
“Wannan miƙa mulkin na da muhimmanci. Kada a yi sakaci da kowa.
“Halastaciyyar hanyar canja gwamnati shi ne ta hanyar zaɓe da aka yi. Duk wata hanya daban ba ta halasta ba kuma saɓa doka ne.”
MURIC ta yi kira ga Datti ya bi tsarin doka ta kuma yi gargaɗi game da yin zanga-zanga kan batun da ake shari’arsa a kotu.