Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Honorabul Muhammed Adamu Bomboy ya ce ya fito neman takarar kujerar Shugaban ƙaramar Hukumar Nasarawa ne domin kawo cigaba a yankin idan aka yi la’akari da yadda ta zama koma baya a wasu ɓangarori na bunƙasa cigaban rayuwar al’ummarta.
Hon. Mohammed adamu (Bomboy) Gama ne ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida akan neman takarar shugabancin ƙaramar hukumar Nasarawa da ya fito.
Ya ce ita dama manufar dimukraɗiyya don matso da gwamnati kusa da mutane ne,musamman a ƙaramar hukuma amma sai gashi ana samun rauni akan haka daga wasu da suka riƙe ƙaramar hukumar a baya.
Ya ce idan aka yi duba da lallacewar harkar Ilimi, lafiya da na tarbiyya na da ɗa ƙamari a tsakanin matasa suna shiga shaye-shaye da harkar daba da ‘yan ɗauke-ɗauke.
Ya ce a fito neman takara shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa ne da kyakkyawar niyyar canza alƙiblar ƙaramar hukumar al’umma su zasu san an sami Gwamnati ta kusa dasu da zata hidimta musu.
Ya yi nuni da cewa wannan takara tasa ba ya fito bane domin ko a mutu ko ayi rai ba, amma yanada burin idan yakai ga nasara zai inganta harkar ilimi don akwai makarantu da dama na furamare da sakandire amma ba zaka iya nuna guda ɗaya a.yankin da ta zama zakaran gwajin dafi ba tsakanin makarantun Model da Sakulala da na islamiyyoyi
Ya ce zai kawo gyara daidai da manufar Gwamnatin Kano na kafa ta dokar ta ɓaci akan ilimi dan sauya tsarin yanda za a haɗa kai da ƙungiyoyi masu zaman kansu a samar da yanayi mai kyau na koyo da koyarwa tsakanin malamai da yan makaranta.
Ya ce a ɓangaren lafiya sunada cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko guda 18. Amma duk cikinsu sun zama kamar wajen yaɗa cuta domin ba kyakkyawan muhallin mai tsafta zama ka iya zuwa ka ɗauki cutar cizon sauro ma a wajen ga banɗakuna ba ruwa wannan gazawa ce babba.
Ya ce za su gyara asibitocin su zama cikin tsafta ya zama wajen neman lafiya.Sanna akwai yara da dama da sukayi karatu a fannin lafiya da yawanci basa aiki za su ɓullo da tsari na haɗin gwiwa da ma’aikatar lafiya ta Jihar Kano yanda za a riƙa ɗaukar su a basu aiki ko da na wucin gadi ne domin ya zama Asibitici a yankin su sami wadatattun masu kulada lafiya a Matakin farko.
Bomboy ya ce zai ƙirƙiro hanyoyin horas da matasa da akan sana’oi da ba su jari su zama masu dogaro dakai da zasu taimaki kansu da yan’uwa da al’umma sannan a ɗorasu akan kyakkyawan tarbiyya da zai kange su daga shaye-shaye da aikata abubuwa da bai kamata ba.
Hon. Mohammed adamu Gama “bomboy”
Ya ƙara da cewa za su dawo da martabar aikin gwamnati a ƙaramar hukumar duk ma’aikaci za a bashi haƙƙinsa da basu horo na sanin makamar aiki domin samun kwarewa na ingancin aiki da riƙo da gaskiya da amana don bunƙasa cigaban ƙaramar hukumar Nasarawa.
