Don ba wa al’adarmu gudunmuwa na ƙirƙiro sababbin abincin gargajiya – Sharif Atiku 

Spread the love

Daga BUSHIRA NAKURA

A daidai lokacin da matasa ke ƙyamatar al’adunsu, da barin duk wata ɗabi’a da za ta iya nuna su ɗin Hausawa ne, sakamakon kallon mai irin ɗabi’ar a matsayin wanda bai waye ba, an samu wani matashi da ke da kishin ƙasarsa ta Hausa, tare da burin haɓaka ta don tafiya da zamani. 

A tattaunawar Blueprint Manhaja da Sharif Atiku, mai karatu zai fa’idantu matuƙa, musamman ma idan ya kasance mai so da sha’awar sanin al’adunmu na Hausa. 

A sha karatu lafiya;

MANHAJA: Assalamu alaikum warahamatullah wabarakatuhu. Mai karatu zai ji daɗi idan ka faɗa mana cikakken sunanka da sunan da aka fi saninka da shi da kuma tarihinka a taƙaice. 

SHARIF ATIKU: Wa alaikissalam wa rahmatullahi wa barakatuh.

Sunana Atiku Abubakar Kabir T/wada, amma kamar yadda ki ka ce; mutane sun fi kira na da Abba ko Sharif Atiku.

Alhamdulillah! Nasami kaina cikin rayuwa daga tsatso mai albarka. Mahaifina Malam Kabiru Dan Shehu Malam Karami na Shehu Atiku Sanka, ya yi hijirar ya da Ilimi, irin ta iyaye da kakanni daga Birnin Kano zuwa garin Ringim da Tudun wada Dankade garin da ya kasance mahaifata a shekarar 1975, bayan tasowa ta na yi karatun Alkur’ani a gida, sai aka saka ni a makarantar boko daga primary School har zuwa secondary GTC T/wada, wadda na kammala sakandare a shekarar 1995, sai kuma na tawo makarantar kiwon lafiya (School of Hygiene, Kano) na fara karatun kula da lafiya tare da tsaftar muhalli (Enɓironmental Health Officer) (EHO), shekara huɗu ne a lokacin amma ban kammala ba saboda wani sharaɗi na Hukumar Jarrabawar lafiya ta Africa (WAHEB) a shekarar karshe, sai na sami ND Certificate na EɓT, bayan kammala karatun da yawan ɗalibai ba mu sami aiki ba a lokacin, sai na fara aiki da Garde (II) a Hukumar Ilimin Bai ɗaya ta Jihar Kano (SUBEB) a Shekarar 2001, don haka na je FCE Kano, domin samun shaidar karatu ta NCE, da ma na fi son harkar karatu da karantarwa, wadda a cikinta na taso yadda Allah ya so kuma ina cikinta har a yanzu, da nake karatun digiri a kan Na’ura mai Kwakwalwa da koyon Aikin Jarida (Computer/ Mass comm.), na yi iyali (aure) da kuma ‘ya daya. Alhamdlillah.

Bayan aikin gwamnati, ko kana da wata sana’a?

A sakamakon bincike da karance karance da kuma rubutu da nake yi, sai naga dacewar na kafa ƙungiya mai zaman kanta (NGO), domin amfanar da al’umma ta kowane ɓangare na rayuwa, don haka na kafa Cibiyar Nazari da yaɗa Ayyukan Kirkira da Fasaha (Al-kausar Multimedia Institute). Alhamdlillah, a ƙarƙashin wannan cibiya mun gabatar da ayyukan cigaban al’umma da kamfanoni da kuma gwamnati a dunƙule.

Malam Abba, kafin bayanin nasarar gudunmawar ka a ɓangaren al’adunmu na Hausa, ko zaka iya faɗa mana irin gwagwarmayar rayuwar da ka sha?

Na’am, kowane mutum ya na da labarin gwagwarmayar rayuwarsa, amma ni labarin da aka bani cewar: “… Mahaifiyata ta rasu a ranar haihuwata…” shine tushen labarin gwagwarmayar rayuwarta, domin labarin ya sani tunani tare da tambayoyin shin : ta yaya zan gane bambancin rashin rayuwa da mahaifiya? A sakamakon banga bambamcin uwa daga wadda ta riƙe ni da sauran Iyaye na Mata ba, kuma duk Matan da nake Mu’amalar Rayuwa da su ina ganin kamanceceniyar kulawa da soyayya irin ta uwa.

Na sami tabbacin haka a ganin yadda nake samun nasarori a cikin duk abinda na ke yi da gudunmawar mata, don haka na umurci ɗalibai na su ƙirkiri amshin waka; akan mahaifiya (Uwa), sai wani Yaro wanda har kyuta na yi masa, shi ya bani amshi kamar haka:

‘Wanda Ya Zamo ɗan Iska Bai More Mahaifiya Ba’

Na bai wa wannan ɗalibi Kyauta ne saboda ya yi gane sakon da na ke son isarwa ta fuskoki biyu:

1. Tun daga amshin waƙar ya yi kule; abinda ake cewa Kalu – bale ga ‘yan uwansa matasa, su zama mutanan kirki don kada su fallasa irin tarbiyyar gidansu ko iyayensu. 

2.Ya yi kule ga uwaye (mata) su ƙara kulawa da tarbiyyar ‘ya’yansu domin ana cewa: “Tarbiyya daga gida take farawa,” musamman a wurin uwa wadda ita tafi zama tare da ‘ya’yanta.

Da fatan kina fahimtata, yawwa. Na bada wadannan labarai 2 don su zama shimfidar saƙo na game da muhimmancin mata a wajen tarbiya da kuma ayyuka na akan al’adarmu ta Hausa.

Addininmu yana da alaka da al’adarmu, don haka matsalar rashin rayuwa da mahaifiya ba ta hana ni cigaba a gwagwarmayar rayuwa ta ba, domin ita ma matsala nasara ce ta wani ɓangaren, kuma Manzon Allah (SAW) ya yi wasiyar a tausaya wa mata, musamman saboda za a iya samun matsala ta ɓangarensu da kuma yiwuwar samun gudunmawa daga gare su, saboda komai raunin mace; to akwai taimakon da take wa al’umma musamman a cikin iyalin da take tare da su. Saboda haka a wannan gaɓa zan so tambayarki ta koma ga ginshikin tattaunawarmu, ta yadda zan yi bayanin gwagwarmayar tabbatar da mata akan al’adunmu na Hausa ta fuskoki dabam dabam.

Menene dalili ko fata da burinku na ƙirƙirar sababbin abincinmu na ƙargajiya?

Dalilai ne da yawa a cikin fata ko buri na kusa da na nesa kamar haka: 1. Bada gudunmawar raya al’adunmu ta fuskar abincinmu na gargajiya da kuma inganta lafiya. 2. ƙarfafawa mata a ƙoƙarin su na riƙe ƙananan sana’o’i domin dogaro da kansu. 3. Bunƙasa ƙasuwancin al’umma da kamfanoni, tare samar da aiki (Employment) ga mata da matasa a faɗin Jihar Kano da ƙasarmu gabaɗaya, musamman ga Hausawa. 4. Shigowa cikin ayyukan fasaha da ƙirkira domin cigaban al’umma. 5. Taimaka wa gwamnati da wakilan al’umma (Representatiɓes) ta wajen sauƙaƙe hanyar tallafa wa al’ummarsu.

A ayyuka biyu da ka ambata a ɓangaren al’adunmu na Hausa, wanne ne dayan?

Ba shi ne na biyu ba, na’am a wannan maganar da kuma lokacin aiwatarwa shi ne muke fatan ya zama na biyu, amma tun farko abinda mu kayi tunani a ɓangaren al’adunmu na Hausa shine: mu ƙirƙiro hanyar raya al’adunmu, sai muka ga ya dace mu fara da Bikin Auren Dala da Goron Dutse, wanda zai zama shine na farko kuma da fatan ya cigaba da maimaituwa a kowace shekara a Jihar Kano insha Allah 

Ya ya za ku yi wannan biki na tarihi, yaushe za ku yi kuma menene ma’anar bikin Auren DALA da Goron Dutse?

Tambaya kwar Uku ko; Uhmn. Zan raba amsoshin gida 3, A. Mun tsara wannan taro zai kasance bikin nuna bajintar dukkan ƙungiyoyin al’adun gargajiyar Hausa kamar haka: Dukawa, Masarauta, Manoma, Masaka, Marina, Masunta, Mahauta, Mafarauta, Masassaka, Majema, Makera, Madinka, Magina, Maharba, Bugo, Wanzamai, Koroso, Amada , Dambe, Kokawa, Langa, Hawan Kaho, Tashe, Shantu, Kalale, Dara, Kidan Buzu, Ranwa/kodi, Yan bori, Mawaƙan Hausa, Hawan Kwara-kwara, Wasan Miciji, Wasan Kura, Goge, ‘Yar Galagala, Shan kankana, ‘Yan Tauri, Shan Kabewa, Mawaka, Hawan Dubar, Wasan Dabe, ’Yar Tsalle, Jau-jau, Wasan Jido. B. ƙungiyar: Kano Annual Hausa Cultural Festiɓal (Bikin Dala da Goron Dutse) a ƙarƙashin Cibiyar Nazari da yaɗa Ayyukan Kirkira da Fasaha (Al-kausar Multidimedia Institute) mun sami sahhalewa daga Gwamnatin Jihar Kano, don haka zamu gabatar da wannan biki na tsawon kwanaki biyu a cikin bikin da Jihar Kano ta shirya mai taken: Kano Festiɓal (KANFEST), saboda haka muna sauraron Gwamnatin Jihar Kano ta sanya lokacin da ya dace. C. Ba biki zamuyi da sunan mun ɗaura aure a tsakanin Dala da Goron Dutse ba, a’a za muyi babban taro na tarihi a matsayin misali na Aron Siffa, somi a aikace ya kasance mun nuna bajintar al’adunmu na Hausa musamman na Jihar Kano, wadda ake yiwa kirari da: Tinjimin gari mai Dala da Goron Dutse.

Menene dalili ko manufar ƙirƙirar wannan bikin gargajiya mai taken Auren Dala da Goron Dutse?

1. Saboda bambance al’adun aro da gyara munanan al’adu, tare da taskace asalin al’adun Hausawa na gari domin yaɗawa da kuma kiyaye tarihi da adabin rayuwar Hausawa a cikin al’adarmu da addininmu. 2. Farkawa da dawowar matasa akan al’adunmu musamman (Dabi’a da Sutura) domin Magabatanmu su yi alfahari da su kuma su zama managarta manyan gobe. 3. Samar da mahada (dandalin) tallata al’adunmu ba tare da bambancin siyasa ko ra’ayi ba, domin kyautata alakarmu da fadada kasuwanci da kuma jawo hankalin masu ziyara mutanan ƙasashen wajen masu yawon buɗe ido (Tourism).

Wacce irin nasara da matsala ka samu a wajen tsarawa da bayyanawa da kuma shirin aiwatar da wannan babban bikin gargajiya irinsa na farko a tarihin Jihar kano.?

Matsala: Kamar yadda na faɗa a sama, kowane mutum akan kowane abu ya zama dole ya sami matsala a tare da nasara a cikin rayuwarsa, har wani lokaci ma ba a iya bambance matsala da nasara saboda ƙarfi da kusancin alaƙarsu. Ni na fara samun matsala ne tun da na fara wayewa da bambancin al’adunmu da na mutanan da ba mu ba ko kuma fifita aladun Bature, sai naga kamar kallo na ake yi na fita dabam. Kuma sai na ci karo da wata agana mai tayar da hankali wadda wani Bature ya bada labarin yadda ya sami kyakkyawar tarbiyyar kakanninmu a ƙasashen Afirka, amma bai yi yabo ba sai ya bada shawarar yadda za a lalata tarbiyyarmu tun kafin wannan zamani da kusan shekaru ɗari biyu, rubutun wanda aka yi cikin harshen Ingilishi yana cewa:

“Na shiga lungu da saƙo a faɗin Afirka, ban taɓa ganin mutum ɗaya mai bara ba, ko ɓarawo ba, duba da irin wannan dukiya da na gani a ƙasar, ga su da wasu irin kyawawan ɗabi’u. Masu irin wannan ɗabi’a, waɗanda ban taɓa gani ba, ina tunanin baza mu taɓa cin nasara a wannan ƙasar ba, sai dai idan har mun karya ƙashin bayan wannan al’ummar, wanda shine Imaninsu da al’adunsu na gargajiya. Ina ba da shawarar mu maye gurbin tsohon tsarin Iliminta, da kuma na al’adunta, har sai ‘yn Afirka sun yi tunanin (amince) cewa duk abinda yake daga Turai shine ya fi nasu kyau da inganci kuma yaren Ingilishi shine mafi girma akan harshensu, da haka ne za su rasa ƙimarsu, al’adunsu na asali kuma za su zama abin da muke so su zama, a ƙarkashin ikonmu.” Jawabin Lord Macaulay ga Majalisar Biritaniya a ranar 2/2/1835.

Wannan ita ce tushen matsala ta wadda ta yi rassa a dukkan matsalolin da zan iya lissafawa, shi ya sa zan takaita ga wannan kaɗai a dunƙule, kuma ita ta sa na dage wajen ƙirƙirar bikin al’adunmu na nishaɗi, wato Auren Dala da Goron Dutse, domin mu kawo gyara ta wannan hanya.

Nasara: Samun wayayyun mutane masu son cigaban Hausawa a cikin al’adunmu da rayuwarmu, na ce Hausawa ne saboda muna batun kyawawan al’adunmu na Hausawa, domin akwai al’adun aro a sakamakon faɗin da yaren Hausa ya yi a duniya, sai bai tsaya a matsayin ƙabilar Hausa ba ƙabilanci bane, a’a yare ne da duk wanda yake ji kuma yake magana da yaren Hausa zai iya amsa sunan Bahaushe, amma asalinsa da al’adunsa za su bambanta shi da mutum haifaffen ƙabilar Hausa.

Akwai nasara a lissafin daidaiku, amma ita ta taƙaita sai dai fatan samun mutane ko ƙungiyoyin da suke kishin al’adunmu da addininmu.

ƙasashe nawa ka taɓa zuwa?

Da yake ba na sha’awar yawo sosai, na fi son kaɗaicewa, amma dai zuwa yanzu na je ƙasashe uku ne.

Jahohi nawa ka taɓa ziyar ta?

A Nijeriya na je jihohi 12.

Yaya kake kallon rayuwar da da ta yanzu?

Rayuwa tana canzawa da cigaban lokaci ko shekaru, a wani lokacin kuma komabaya ne, ko da ana faɗar cigaba a baki ko kuma ana ganinsa a zahiri, saboda ba a bin ƙa’idojin rayuwar ko domin a rayu. Amma dai dole a kowane hali a kwai yanayi da sai anyi fito na fito (gwagwarmaya) tare da kyautata aiki domin fuskantar matsalolin rayuwar duniya da kuma rayuwar lahira.

Ko kana da wani buri da ka ke son cikawa ?

Na’am, kowane mutum yana da buri na kusa da na nesa, amma da yawa ba kowanne buri ne ya ke samuwa ba, saboda Manzon Allah (SAW) ya taɓa rubutawa Sahabbansa wani zane mai kusurwa huɗu, a cikinsa da zanen kibiyoyi; ya ce bala’o’i ne da ke fuskantar mutum a kan layin ajalinsa guda biyu (layin) ya zarce kusurwa huɗin ta Gabas da Yamma da Kudu da Arewa, wadda su ne gaɓar ajali, da ake cimma sa kafin cikar wannan buri.

Amma ni babban burina shine Allah ya karɓi ayyukanmu a cikin abinda ya bayyana da na ɓoye, idan kuma ajali ya zo mu cika da imani, kuma a sami wani ko wasu su cigaba daga inda muka tsaya.

Wacce shawara za ka bai wa mutane da shugabanni?

Mutane mu ne bayin Allah, a cikinmu ajin shugabanni ke samuwa tare da masu taimaka musu (malamai da attajirai). Ya zama dole attajirai/shugabanni su tuna Manzon Allah (S) yana cewa: Allah ya ce: ” Dukiya tawa ce, mutane Iyali na ne, masu kuɗi kuma wakilai na ne, duk wanda ya hana iyalina (mutane) dukiya ta; to zan saka shi a cikin wuta ta ba tare kulawa ba.” Don haka duk ɓangarorin nan ya zama dole mu rayu a cikin fahimtar juna da taimakekeniya a tsakaninmu tare da biyayya da kuma jagoranci na Blbiyar Allah, da haka ne kaɗai za mu tsira gaba dayanmu a duniya da lahira.

Fatanka ga jaridar Blueprint Manhaja?

Mun yi farin cikin samuwar wannan jarida (Blueprint) Allah ya ƙara mata karɓuwa da ɗaukaka, kuma ina fatan zata wakilci Hausawa.

Godiya Allah (T) mara adadi, da fatan samun nasara daga gare shi alfarmar Annabi Muhammad (SAW).

Ni ma na gode.

By ukarofi