Don sauƙaƙa wa al’umma KACCIMA za ta yi bajekolin kayan abincin azumi – Sidiya Yako    

Spread the love

Daga MUHAMMAD MUJITABA a Kano

Shugaban ƙungiyar AFAN ɓangaren mata manoma kuma shugabar ƙungiyar mata manoma da sarrafa amfanin gona ta Kano, Hajiya Fatima Sharu Gambo Yako, ɗaya daga cikin ‘yar kwamitin shirya bikin bajekolin kayan abincin azumi da cibiyar ciniki da masana’antu ma’adanai da aikin gona wato Kano Chamber of Commerce Mines and Agriculture (KACCIMA) ta shirya, Sidiya ta ce wannan bajekoli ya ƙunshi kayan amfanin gona kamar irinsu shinkafa, wake, dawa, masara, gyaɗa, manja, man gyaɗa, doya, ƙwai da sauran kayayyaki da masa’antu da kamfanoni suke sarrafawa duk za a baje su a wannan bajekoli da KACCIMA ta shirya a wannan lokaci.

Haka kuma Hajiya Fatima Sharu Gambo Yako, ta yaba wa gwamnan Kano kan yadda ya ɗada sabon kwamishinan ciniki da masana’antu na jihar Kano Alhaji Wada Sagagi wanda yake da kyakkyawar alaƙa da wannan cibiya da ‘yan kasuwar Kano baki ɗaya da kuma yadda ya yi ruwa ya yi tsaki wajen ganin wannan bajekoli ya yi nasara ta hanyar ganin al’umma ta samu sauƙin kayayyakin amfani da azumi da ma bayan azumi a cewar Sidiya Sharu Gambo Yaƙo.

A ƙarshe ta yi kira ga kamfanoni da manoma da ‘yan kasuwa da sauran al’umma su halarci wannan kasuwa domin bajekolin kayansu ko kuma samun kaya cikin sauƙi domin amfanin azumi a wannan wata na Ramadan mai kamawa nan da ‘yan kwanaki masu zuwa in da kuma ta yaba wa shugabanni da ɗaukacin ma’aikatan wannan cibiya ta KACCIMA da ke birnin Kano.  

By ukarofi