
Daga BELLO A. BABAJI
Hukumar Kiyaye Haɗurra (FRSC) reshen Jihar Kano, ta ce kimanin mutane 23 ne suka rasa rayukansu da kuma wasu guda 48 da suka jikkata a yayin wani hatsari da ya auku a gadar Muhammadu Buhari dake Hotoro a Kano.
Kakakin hukumar, CRC Abdullahi Labaran ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Juma’a inda ya ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis a hanyar Kano zuwa Maiduguri, da misalin ƙarfe 9:50 na dare.
Ya ce, jami’an agajin gaggawa na rundunar da haɗin-gwiwar ƴan sanda ne suka hanzarta zuwa wajen da abin ya faru da ceto mutane gami da warware matsalolin cinkoso a yankin.
Lamarin ya auku ne a lokacin da wata tirela ɗauke da mutane da wasu kayayyaki ke tuƙi cikin hanzari, inda daga nan burkinta ya ƙwace a ƙarƙashin gadar, wanda ya yi sanadiyar asarar rayuka da dukiyoyi, kamar yadda ya bayyana.
Ya ƙara da cewa, Nan da nan aka garzaya da waɗanda suka samu raunukan zuwa asibitin Murtala dake jihar don ba su kulawa.
A nasa jawabin, Shugaban rundunar, CC UM Matazu ya ce sun aika wata tawaga ta musamman domin gudanar da ƙwaƙƙwaran bincike game da hatsarin.
Ya kuma gargaɗi direbobi da ɗaukacin al’umma da kiyayi sanya wa tireloli mutane ko dabbobi ko wasu kayayyaki sama da kuma waɗanda hakan a lokuta da dama suke sabbaba hatsari.
