Drogba ya musanta karɓar addinin Musulunci

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafar Ivory Coast, Didier Drogba ya musanta labarin da ke cewa ya karɓi addinin Musulunci.

Wannan na zuwa ne bayan da wani malami ya wallafa hotonsa tare da tsohon ɗan ƙwallon suna addu’a a shafinsa na Tuwita.

Kotu Ta Daure Barawon Awaki A Gidan Kaso
Malamin ya wallafa hoton, tare da cewa tsohon ɗan ƙwallon ya musulunta.

To sai dai a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, Drogba ya ce ba musulunta ya yi ba, addu’a kawai ya ke yi wa musulman ƙauyensu bayan da ya ziyarci ƙauyen nasu.

Ya bayyana cewa, “ba musulunta na yi ba lokaci ne na nuna ’yan uwantaka.”

Daga baya malamin mai suna Mohamed Salah ya goge saƙon da ya wallafa ɗin, inda ya ce Drogba ba musulunta ya yi ba, to amma kuma zai cigaba da yi masa addu’ar musulunta.

By Editor