Kamfanin Sin ya haskaka ƙauyen Lauteye na Jihar Kanon Nijeriya

Daga FA’IZA MUSTAPHA

Hasken lantarki, muhimmin ɓangare ne na ababen more rayuwar ɗan Adam, musammam a wannan zamani da muke ciki da komai ke da alaƙa da hasken lantarki.

Tsayayyen wutar lantarki ko akasinsa, wani mizani ne na auna ci gaban wuri.

Don haka, samun wutar lantarki daga makamashi mai tsafta, wani karin tagomashi ne ga rayuwar bil adama da muhalli.

Na yi wannan shimfida ne bisa la’akari da gagarumar gudunmawar da kamfanin PowerChina ya bayar a baya-bayan nan, inda ya gwangwaje ƙauyen Lauteye na yankin ƙaramar hukumar Bunkure ta jihar Kano dake Arewa maso yammacin Nijeriya, da na’urori 500 na samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana.

Samun wannan labari, ya yi matukar faranta min rai, ganin yadda wani mutumin yankin mai shekaru sama da 40, ya ce ƙauyen nasu bai taba samun hasken lantarki ba.

Haƙiƙa wannan yunƙuri na kamfanin ƙasar Sin zai taimakawa al’ummar ƙauyen, ta hanyoyi daban-daban.

Misali, za a samu ingantuwar tsaro, harkokin kasuwanci za su bunƙasa, ɗalibai za su ƙara samun damar bitar karatunsu, al’umma za su samu damar more fasahohin zamani, kana za su daina kashe kudin sayen gawayi ko kalanzir ko ƙyandir da sauransu, haka kuma, ina da yakinin ya buɗe wa ƙauyen wani sabon babi na ci gaba.

Yunƙurin wani ɓangare ne na shirin kamfanoni 100 a kauyuka 1,000, wanda ƙungiyar ’yan kasuwar ƙasar Sin a Afrika ta ƙirƙiro, da nufin tattara kamfanoni ƙasar Sin 100, domin su aiwatar da ayyuka 1,000 da al’ummomin nahiyar za su ci gajiyarsu.

Baya ga taimakawa wajen bunƙasa tattalin arzikin nahiyar da samar da guraben ayyukan yi da gudanar da ayyukan agaji, kamfanonin ƙasar Sin suna ƙoƙarin tallafawa al’ummomin ƙauyuka da ba kowa ne zai tuna da su ba.

Shi ya sa a kullum na kan ce, ƙasar tana da hangen nesa da sanin ya kamata, domin na tabbata, mutanen ƙauyen da ma jihar Kano, har da ƙasarmu ba za su manta da irin taimakon da Sin ba.