APC ta naɗa Kannywood cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu/Shettima

Daga BASHIR ISAH

Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC kuma Gwamnan Jihar Filato, Simon Bako Lalong, ya amince da naɗin masana’antar shirya fina-finai a Arewacin Nijeriya, Kannywood a matsayin mamba a kwamitin PCC.

Naɗin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Sakataren yaɗa labarai da mu’amala da jama’a ga Gwamnan Lalong, Dr. Makut Simon Macham, kuma mai ɗauke da kwanan wata 8 ga Nuwamba, 2022.

Gwamna Simon Lalong

Sanarwar ta ce, naɗin ya biyo bayan tabbacin da ɗan takarar Shugaban Ƙasa a APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bai wa masana’antar ta Kannywood yayin wani taro da ya halarta a Kano inda ‘yan masna’antar suka tabbatar masa suna tare da shi.

Bayan baje fasaharsu da ‘yan Kannywood ɗin suka yi a gaban ɗan takarar a wannan rana, ya sa ya yi musu alƙawarin samar musu gurbi a Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓensa don tallafa masa wajen cimma burinsa na shugabancin ƙasa.

Yayin da ‘yan Kannywood ke nishaɗantar da taron da aka yi a Kano

Shugaban PCC, Gwamna Simon Lalong, ya bauƙaci ‘yan masana’antar su tattaro masoyansu don a haɗu a mara wa ɗan takararsu baya, tare da kira gare su da su ba da himma wajen tallata Asiwaju da manufofinsa ga ‘yan ƙasa yadda ya kamata.

‘Yan tawagar Kannywood ɗin sun haɗa da Abdul Moh’d Amart a matsayin Darakta da Ismail Na’abba Afakallah a matsayin mataimakin Darakta, sai Sani Mu’azu a matsayin Sakatare da sauransu.