Gwamnatin Kano za ta maka Sahara Reporters a kotu idan ba ta janye rahotonta, ta ba Ganduje haƙuri ba – Kwamishina

Daga AMINA YUSUF ALI

Gwamnatin jihar Kano ta nemi jaridar Sahara Reporters (SR) da ta ba ta haƙuri kuma sannan ta janye rahotonta a kan Ganduje.

Bayan sakamakon rahoton EFCC ya wanke gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje a kan rahoton da jaridar ta wallafa cewar yana daga gwamnonin Nijeriya waɗanda EFCC ta kasafta a jerin waɗanda suke voye Naira a gidajensu.

Hakazalika, gwamnatin jihar Kano ta yi zazzafan Allah wadai ga wani rahoto da jaridar yanar gizon mai suna SR, cewar Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje yana cikin jerin gwamnoni guda uku da suke ɓoye Nairori a gidajensu.

A wani jawabi na Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba ya bayyana cewa, tabbas hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta yi dungu ne, ba ta ambaci sunayen gwamnonin da take zargi da voye kuɗin ba, amma ita jaridar ta SR sai kawai ta shato sunayen da ta ga dama ta faɗa. Wanda a cewar sa, ƙarya ce tsagwaronta.

A cewar sa, wannan rahoto wanda sam ba a yi bincike ba, kafin a gudanar da shi, ko dai hasashen mawallafin ne, ko kuma da gangan aka yi don a yi ɓatanci ga Gwamna Ganduje.

Malam Garba ya ƙara da cewa, sam gwamna Ganduje bai voye waɗancan biliyoyin kuɗaɗe da ake zargi ba a gidansa. Har ake zargin zai yi wa ma’aikata biyan albashi na hannu-da-hannu a wannan zamani na hada-hadar bankin yanar gizo.

Kwamishinan ya ƙara da cewa, jihar Kano tana ɗaya daga cikin ƙalilan ɗin johohin da suke biyan ma’aikata albashi a kan kari. Kuma ko a lokacin da jaridar ta saki wancan rahoton na vatanci, gwamnatin tuni ta jima da biyan albashi ma’aikatanta watan Oktoba.

A kan haka ne ya nemi da su janye wannan labarin sannan mawallafin ya ba da haƙuri ga gwamnatin Kano, rashin ba da haƙuri, zai iya sa gwamnatin ɗaukar matakin Shari’a, a cewar sa.