Yadda rokokin sojojin Nijeriya suka hallaka shugabannin ISWAP, Ali Kwaya da Bukar Mainoka a Chadi

Daga AMINA YUSUF ALI

Wasu ƙasurguman shugabannin mayaƙan ISWAP, Mallam Ali Kwaya da Mallam Bukar Mainoka, sun haɗu da ajalinsu a hannun jami’an sojin Nijeriya a tafkin Chadi, ranar Asabar ɗin da ta gabata.

Dubun Kwaya da Mainoka, waɗanda kuma manya ne a majalisar Shura ta ISWAP ta cika ne a lokacin da tawagar sojin sama ta ‘Operation Hadin Kai’ ta kai musu samame a garin Belowa.

Mamatan biyu suna daga cikin ƙalilan ɗin mayaƙan ISWAP/Boko Haram da suka yi saura a boye a yankin Tumbuns, dake tafkin Chadi a ƙaramar hukumar Abadam.

Majiyarmu ta bayyana cewa, Sojojin Nijeriya sun ga ya zama dole a kai samamen ne saboda sakamakon bayanan sirrin ya bayyana cewa akwai wasu shugabannin mayaqan ISWAP da suke a waɗannan yankunan, kuma suna da niyyar kai farmaki ga jami’an tsaron.

Kuma a cewar rundunar sojin na sama, sun boye kansu ne a maɓoyansu a yankin Belowa. Daga nan suka cigaba da sakin rokoki da bama-bamai ba ji, ba gani.

Bayan samun awannin 2 ana luguden wutar ne kuma aka hangi motoci biyu ɗauke da kusan raunatattun ‘yan ta’addan guda 13 kuma wannan aman wutar shi ya tursasa suka bayyana.

Rahotannin bayan ƙaddamar da harin ne suka bayyana yadda manyan ‘yan ta’addan Mallam Ali Kwaya wanda shi wani jigo ne a majalisar shurar ISWAP da kuma Mallam Bukar Mainoka suka cimma ajalinsu.

Jami’an sojin sun bayyana cewa, sun gudanar da makamancin wannan farmakin a ranar Juma’a ma a yankin Ngwuri Gana a ƙaramar hukumar Bama ta gabashin Maiduguri.

Rahotanni sun bayyana cewa, an cimma nasara a samamen domin an hallaka ‘yan ta’adda da dama sannnan an ƙone musu ababen hawansu da dama a wannan harin.

Mai magana da yawun rundunar Sojojin saman Kwamanda Edward Gabkwet, ya tabbatar da faruwar al’amarin sai dai kuma ya kame bakinsa ga ƙin kama sunayen waɗanda aka kashe ɗin.

Ya ƙara da cewa, “ba gudu ba ja da baya, a Arewa maso yamma, da Arewa maso gabacin Nijeriya ba za mu gajiya ba, har sai mun tabbatar an shafe ta’addanci daga waɗannan wuraren”.