DSS da EFCC suna binciken kamfanin Chana bisa zargin damfara

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Manyan hukumomin tsaro da yaƙi da cin hanci na Nujeriya sun fara gudanar da bincike kan wani kamfanin ƙasar Chana mai suna Eɗcel-LED bisa zargin karɓar kuɗin kwangilar allunan nuni na filayen jiragen sama na sama da Naira miliyan 100 ba tare da cika alƙawarin aikin ba.

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC, tare da Hukumar ICPC mai yaƙi da cin hanci a ma’aikatu, na binciken kamfanin, Manajan Daraktansa Sam Lee wanda ake zargin yana amfani da sunan Emmanuel Shoon Patrick, da rassan kamfanin na Eɗel LED Optoelectronics da Adsen, tare da wani ɗan Nijeriya mai suna Ndubisi.

Rahotanni sun nuna cewa binciken ya biyo bayan wata ƙorafi da kamfanin lauyoyi na Anosike, Egbuchiwe and Associates ya shigar a ranar 22 ga Disambar 2025 a madadin kamfanin Folio Media Group.

Taƙaddamar ta samo asali ne daga wata yarjejeniya ta samar da manyan allunan nuni na zamani domin filayen jiragen sama na Enugu, Fatakwal da wasu filayen jiragen sama na ƙasa da ƙasa. Kamfanin Folio Media ya bayyana cewa an shirya amfani da allunan wajen nuna tallace-tallace da bayanan zirga-zirgar jirage domin samar da kuɗaɗen shiga.

A cewar takardar ƙorafin, an fara tura kuɗaɗen farko zuwa asusun kamfanin na ƙasar Chana, inda aka kawo alluna uku na farko. Sai dai ɗaya daga cikin allunan bai wuce gwajin inganci ba, lamarin da ya sa aka ajiye shi tsawon watanni shida a filin jirgin saman Enugu ba tare da amfani ba, abin da ya janyo asarar kuɗaɗen shiga.

Daga bisani, an sake bai wa kamfanin damar ci gaba da aikin. Sai dai a mataki na ƙarshe, an karkatar da biyan kuɗaɗen zuwa asusun bankin Emmanuel Shoon Patrick da ke Nijeriya, bisa hujjar kuɗin kwastom da jigilar kaya. Rahoton ya nuna cewa a ranar 4 ga Disambar 2025 an tura wani babban adadin kuɗi zuwa asusun nasa.

Kamfanin Folio Media ya yi zargin cewa Patrick, wanda ake zargi ya gabatar da kansa a matsayin Shugaban Kamfanin Eɗcel-LED Nigeria Limited, ya karɓi kuɗin sannan ya tafi ƙasar Chana ba tare da kawo kayan ko mayar da kuɗin ba.

Bayanan wuraren aiki sun nuna cewa babu wata kaya da aka sake kawowa bayan an karkatar da kuɗin zuwa asusun nasa, yayin da ƙungiyoyin masu girka kayan suka kasa halartar lokutan da aka tsara musu sau da dama.

Rahotanni sun ce jami’an EFCC sun gano Sam Lee da Ndubisi a Fatakwal kafin daga bisani suka kai su Abuja domin amsa tambayoyi, bayan sun yi watsi da gayyatar da aka yi musu tsawon kusan watanni uku.

Takardar ƙorafin ta buƙaci DSS, ICPC da EFCC su binciki zargin damfara, kauce wa biyan haraji da kuma yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa.

Lauya Max Uchendu ya bayyana cewa karkatar da kuɗaɗe zuwa asusun mutane maimakon na kamfanoni na taimakawa wajen kauce wa biyan harajin ɓAT da sauran kuɗaɗen gwamnati, abin da ya ce na haddasa asarar biliyoyin nairori ga Nijeriya musamman a ayyukan fasahar zamani da sadarwa.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wani daga cikin waɗanda ake zargi da ya fito fili domin mayar da martani kan zarge-zargen da ake musu.

By ukarofi