Kebbi: Jami’an Hizba sun kama mutum ya ɓoye cikin jaka a ɗakin matar aure

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Jami’an hukumar Hisbah da ke ƙarƙashin hukumar kula da harkokin addini a Kebbi, sun kama wani mutum da ya ɓuya a jakar “Ghana Must-Go” a ɗakin wata matar aure mai suna Badariya a Birnin Kebbi.

Daraktan shari’a a hukumar, Sirajo Kamba, ne ya tabbatar da kama mutumin a cikin jawabin da ya aike wa kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) a ranar Talata a Birnin Kebbi.

A cewar Kamba, mazauna unguwar ne suka sanar da Hisbah da misalin ƙarfe 12:15 na dare a ranar Litinin, 18 ga watan Mayu, bayan sun lura da wani mutum da ya shiga gidan wata mata.

“Mazauna unguwar sun ce sun yi zargin akwai wani abu da ya saɓa wa addini da ke faruwa a gidan wanda ya sa suka sanar da hukumar.”

“Bayan samun rahoton, hukumar Hisba a Kebbi ta tura jami’anta domin su gudanar da bincike.”

“A lokacin da jami’an suka je, sun samu izinin binciken gidan, sai dai matar gidan da farko ta ƙi barin kowa ya shiga gidan,” ya faɗa.

Daraktan, ya ce, daga baya matar an tilasta mata inda ta bari suka shiga wanda ya jawo suka gano wanda ake zargi a jakar ‘Ghana Must-Go’.

Ya ƙara da cewa bayan ƙara yin bincike zai suka gano akwai alaƙar soyayya tsakanin mutumin da matar auren.

Kamba ya ce, bayan yi wa dukkansu tambayoyi, dukkansu sun amince da cewa akwai alaƙar soyayya a tsakaninsu.

Ya ƙara da cewa waɗanda ake zargin za a gurfanar da su a gaban kotu domin fuskantar hukunci.

By ukarofi