Rundunar Sojin Nijeriya ta ƙaryata zargin ’yan ta’adda sun kafa sansanin dindindin a Kudu maso Yamma

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shalkwatar tsaron Nijeriya (DHƙ) ta musanta rahotannin da ke cewa ’yan ta’adda sun kafa sansani na dindindin a yankin Kudu maso yammacin Nijeriya, tana mai bayyana harin da aka kai makarantu da sace ɗalibai da malamai a jihar Oyo a matsayin wani keɓantaccen aikin ta’addanci saboda babu wata shaida ta nuna akwai ƙungiyar ta’addanci a yankin.

Mai magana da yawun rundunar tsaron, Michael Onoja, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

Ya ce Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Olufemi Oluyede, ya jajanta wa iyalan wadanda aka sace da gwamnatin jihar Oyo da ɗaukacin al’ummar Nijeriya kan lamarin.

A cewar sanarwar, sace yara ƙanana da malamai makaranta mummunan abu ne da ya girgiza zukatan ’yan Nijeriya bakiɗaya. Rundunar sojin Nijeriya ta tabbatar da cewa tana amfani da dukkan karfinta da dabarunta wajen ganin an kuɓutar da wadanɗa aka sace ba tare da wani sharaɗi ba.

Shalkwatar tsaron ta buƙaci ’yan Nijeriya su kwantar da hankalinsu tare da bai wa jami’an tsaro haɗin guiwa ke farautar masu garkuwa da mutanen.

A baya dai an ruwaito cewa wasu ’yan bindiga sun kai hari makarantu biyu a yankin ƙaramar hukumar Oriire ta jihar Oyo, inda suka sace aƙalla mutane 45 da suka haɗa da ɗalibai da malamai.

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya tabbatar da afkuwar harin, yana mai cewa ɗaya daga cikin malaman ya rasa ransa yayin harin.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun tafi da waɗanda suka sace zuwa cikin dajin tsohon filin shaƙatawa na Oyo wanda wani babban daji da ke yankin.

Sai dai gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa a shirye take ta shiga tattaunawa da masu garkuwa da mutanen domin ganin an sako waɗanda aka sace lafiya.

Lamarin ya jawo martani daga ’yan Nijeriya da dama, inda wasu ke bayyana fargabar cewa ’yan ta’adda sun fara kafa sansani a yankin Kudu maso yamma.

Bayanan sirri sun nuna cewa babu wata hujja da ke tabbatar da cewa akwai sansanin dindindin na ’yan ta’adda a yankin.

A cewar Mista Onoja, rundunar soji ta taba kai manyan hare-hare kan masu aikata laifi a yankin Old Oyo National Park, inda aka karya lagon ƙungiyoyin masu aikata laifi da ke aiki a yankin.

Saboda haka, ya ce sabon harin da aka kai bai nuna cewa akwai wata cikakkiyar ƙungiyar ta’addanci da ta kafa tushe a yankin.

Shalkwatar ta kuma gargaɗi mutane da su guji yaɗa labarai da za su haddasa tsoro ko kuma su ƙara wa masu aikata laifi ƙarfin guiwa ta hanyar nuna su kamar sun fi karfin rundunar sojin ne.

Sanarwar ta ƙara da cewa sojoji sun bazama cikin dazukan yankin domin nemo wadanda aka sace da kuma cafke masu garkuwa da mutanen.

Ta ce jami’an tsaro sun yi artabu da maharan kwanaki biyu da suka gabata, kuma yanzu haka sun sake tsara dabarun ci gaba da farautar su.

Hakazalika, ana gudanar da ayyukan haɗin guiwa na tsaro tsakanin sojoji da sauran hukumomin tsaro da kuma ƙungiyoyin sa-kai na yankin domin mamaye hanyoyin dazuka da wuraren da ba su da cikakken ikon gwamnati.

Shalkatar tsaron ta jaddada muhimmancin haɗin kan al’umma wajen tattara bayanan sirri, tana mai cewa bayanan da mazauna yankuna ke bayarwa na da matuƙar amfani wajen kuɓutar da wadanda aka sace cikin gaggawa da kuma tabbatar da tsaron yankin bakiɗaya.

By ukarofi