DSS sun cafke budurwar da ta yi wa Shettima da Gawuna barazanar ƙunar baƙin-wake

Spread the love

Jami’an DSS a Kano sun cafke Fiddausi Ahmadu, ‘yar shekara 23, bayan da ta yi barazanar ƙunar baƙin-wake a kan waɗanda ta ce suna da hannu a nasarar da Jam’iyyar APC ta samu a shari’ar zaɓen gwamnan Kano a Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe.

Majiya mai tsushe ta tabbatar wa jaridar News Point Nigeria da batun kama budurwar da DSS ta yi da safiyar Talata.

Majiyar ta ce Fiddausi na iƙirarin taya Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusu da jam’iyyarsa ta NNPP faɗa ne kamar yadda aka gani a cikin wani faifan bidiyon da aka yaɗa.

An ji Fiddausi a cikin bidiyon na farmakin alƙalin da ta jagoranci shari’ar a kotun, tana mai cewa duk inda ta haɗu da ita za ta rungume ta su mutu tare.

Haka nan, an ji lokacin da take gargaɗin Gawuna tana cewa muddin ta gano inda yake za ta bi shi ta tayar da bom.

Kazalika, ta yi amfani da bidiyon wajen yi wa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, barazana tare da zarginsa da hannu cikin hukuncin da kotun ta yanke na soke nasarar Gwamna Abba.

A cewar majiyar, “Lallai za mu gurfanar da Fiddausi Musa Ahmadu a kotu saboda bai kamata a ɗauki barazanar da ta yi da wasa ba.”

By Editor