Rushewar ginin coci ta yi ajalin Fasto a Binuwai

Spread the love

Bayanin da muka samu yanzu-yanzu ya ce, sashen ginin Cocin Dunamis da ke daura da Mission Ward North Bank a Makurɗi, babban birnin Jihar Binuwa, ya rushe.

Blueprint Manhaja ta kalato cewar, rushewar ginin wadda ta auku da safiyar wannan Talatar ta yi ajalin wani fasto tare da jikkata wasu masu ibada a mujami’ar.

Bayanai sun ce, Faston tare da wasu mutum uku na tsaka da gabatar da addu’a ne a lokacin da wani ɓangaren ginin ya rikito a kansu.

Ya zuwa haɗa wannan labari babu cikakken bayani kan dalilin aukuwar iftila’in.

Da aka nemi jin ta bakinta, Kakakin ‘yan sandan jihar, Anene Sewuese Catherine, ta ce ba ta da masaniya a kan haka.

Sai dai, tuni jami’an ‘yan sanda
na C Division da ke yankin tare da wasu jami’an bada agajin gaggawa sun hallara wurin da abin ya faru don ba da taimakon gaggawa.

By Editor