DSS za ta ɗaukaka ƙara bisa yanke hukuncin ɗauri kan masu garkuwa da ɗaliban Oyo 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa wasu mutum uku hukuncin ɗaurin rai da rai bayan sun amsa laifukan da suka shafi garkuwa da ɗalibai da malamai a ƙaramar Hukumar Oriire ta Jihar Oyo.

Sai dai Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta bayyana rashin gamsuwarta da hukuncin, tana mai cewa za ta ɗaukaka ƙara domin neman a yanke musu hukuncin kisa, saboda girman laifukan da suka aikata.

Mai shari’a Salim Ibrahim ya yanke wa Abdulrazak Umar wanda aka fi sani da Abu Khalifa ko Abu Khalid, Yunusa Musa (Yunusa Bin Musa), da Shamsu Adamu Sani (Abu Itisar) hukuncin ɗaurin rai da rai, wanda zai fara aiki tun daga ranar da aka kama su.

Waɗanda aka yanke wa hukuncin sun amsa cewa su mambobi ne na ƙungiyar Darul Salam, wadda ke da alaƙa da ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru. Sun kuma amsa laifin ɓoye bayanai kan shirin satar mutane da kuma yaɗa ra’ayoyin da ke ƙarfafa ta’addanci.

Abdulrazak Umar shi kaɗai ya amsa ƙarin tuhume-tuhume da suka haɗa da horas da mambobin ƙungiyar, ba da umarnin gudanar da ayyukan ta’addanci da kuma ƙarfafa mabiyansa ta hanyar wa’azi.

Lauyan waɗanda aka yanke wa hukuncin ya roƙi kotun ta sassauta musu hukunci, yana mai cewa su ne karo na farko da suka aikata laifi, sun nuna nadama kuma suna da iyalai da suka dogara da su.

Sai dai lauyan DSS ya buƙaci kotun ta yi hukunci mai tsauri, yana mai cewa waɗanda ake tuhumar sun san ayyukan ta’addanci da masu aikata su amma suka ƙi sanar da hukumomin tsaro.

Kotun ta yanke wa mutum ukun hukuncin ɗaurin rai da rai kan laifin da ke cikin ƙidaya ta shida, sannan ta ƙara yanke wa Abdulrazak Umar hukuncin ɗaurin rai da rai kan wasu ƙarin tuhume-tuhume da suka shafi horas da ‘yan ta’adda da yaɗa umarnin gudanar da ayyukansu.

Duk da samun nasarar shari’ar, DSS ta ce hukuncin bai dace da girman laifin ba, musamman ganin cewa an kashe malamai biyu ta hanyar fille kansu yayin harin satar ɗaliban.

Hukumar ta ce za ta ɗaukaka ƙara zuwa kotun daukaka ƙara domin neman a ƙara tsaurara hukuncin.

Haka kuma DSS ta tuna cewa a makon da ya gabata ma za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin ɗaurin rai da rai da aka yanke wa wasu manyan jagororin ƙungiyar Ansaru biyu, tana mai jaddada cewa hukuncin laifukan ta’addanci ya kamata ya zama mai tsanani domin ya zama izina ga masu aikata irin waɗannan laifuka.

By ukarofi

Leave a Reply