Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF) ta bayyana damuwarta kan yadda Gwamnatin Jihar Legas ta rufe idanunta wajen rushe kasuwar Alaba Rago, inda ta yi gargaɗin cewa matakin ya sanya dubban ‘yan kasuwa sun afka asara da kuma jefa iyalai cikin halin ƙunci na matsin rayuwa.
Kasuwar da ke ƙaramar Hukumar Ojo a jihar Legas, wuri ne da dubunnan ‘yan kasuwa, musamman Hausawa daga Arewa ke kasuwanci.
A wata sanarwa da kakakin ACF na ƙasa, Farfesa Takur Muhammad-Baba, ya fitar ranar Laraba, ƙungiyar ta ce, wannan mataki ya haddasa asarar kadarori da tsanantar talauci ga ’yan kasuwa.
An fara rushe kasuwar ne dagar ranar Lahadi, 17 ga Agusta, har zuwa Laraba, 20 ga Agusta.
Wannan rushe-rushe ya raba ɗaruruwan ’yan kasuwa da wurin sana’arsu, inda suke samun damar rufa wa kansu asiri.
Kasuwar dai ta shafe kusan shekaru 50 a matsayin cibiyar cinikin kayan abinci, dabbobi da kuma sauran kayan bukatu.
Sanarwar ta ce, “Rushe wannan kasuwa mai ɗimbin tarihi ya jawo durƙushewar kasuwanci da kadarori, tare da rushe hanyoyin samun abinci ga dubunnan mutane.”
ACF ta bayyana jin daɗinta ganin cewa babu asarar rayuka da aka yi a yayin rushewar, sannan ta yi jaje ga waɗanda abin ya shafa.
ƙungiyar ta ce, “Muna sa ran juriya da aka san jama’an Arewa da shi za ta taimaka wa ‘yan kasuwar wajen fuskantar ƙalubalen asarar da su ka yi.”
ƙungiyar ta ƙara da cewa, ta fara tattara cikakkun bayanai kan abin da ya faru da dalilan da suka haifar da shi, tare da shirin tattaunawa da hukumomi da al’ummar da abin ya shafa.
ACF ta kuma yi kira ga gwamnatin jihar Legas da gwamnatin tarayya da su ɗauki matakan gaggawa na kawo taimako da tallafi ga waɗanda suka yi asara.
