Dujiman Katsina ya yi ta’aziyar rasuwar Jakada Zakari Ibrahim

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Dujiman Katsina kuma shugaban kwamitin harkokin cikin gida na majalisar wakilai Hon Aliyu Abdullahi ya bayyana rasuwar Talban Katsina a matsayin babban rashi ba wai al’ummar jihar Katsina ba har da ƙasa baki ɗaya.

A wata takardar sanarwar ɗauke da sa hannun mataimaki na musamman a kan yaɗa labarai Mr Francis Sardauna ya ce ɗan majalisar ya ɗimauta ƙwarai da samun labarin rasuwar Jakada Zakari Ibrahim.

Ya bayyana marigayi Talban Katsina a matsayin ɗaya daga cikin manyan jami’in tsaro a ƙasan da ya ɗaukaka darajar jihar Katsina a idon duniya.

Dujiman Katsina ya ƙara da cewa duk cigaban da jihar Katsina ta samu tun lokacin da aka sami jihar zuwa yanzu akwai gudunmawar marigayi Talban Katsina.

“Marigayi Talban Katsina ya samarwa matasan jihar Katsina da aikin yi a ma’aikatun gwamnatin tarayya a mataki daban daban, ga kuma tallafawa marasa ƙarfi “ɗan majalisar yace.

Hon Aliyu Abdullahi ya yi addu’ar Allah masa rahama, ya yafe masa kurakuransa, ya ba iyalan sa da al’ummar jihar Katsina haƙurin juriyan babban rashi da aka yi.

Marigayi Talban Katsina Jakada Zakari Ibrahim ya riƙe muƙamin shugaban hukumar tsaro ta NIA a lokacin mulkin Jana Sani Abacha da Goodluck Jonathan kafin daga baya ya riƙe muƙamin ƙaramin ministan harkokin waje.

Gwamnan Jihar Katsina malam Dikko Raɗɗa da mai martaba Sarkin Katsina Alhaji (Dr) Abdulmummuni Kabir Usman da tsohon ministan sufuri sanata Hadi Sirika da sauran ɗaruruwan mutane suka halarci jana’izar sa da ta gudana a fadan sarkin Katsina.

Ya rasu yana da shekara 81 a duniya

By ukarofi