Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Dikko Raɗɗa da mai martaba sarkin Katsina Alhaji Abdulmummuni Kabir Usman na daga cikin waɗanda suka halarci jana’izar Talban Katsina.
Sauran waɗanda suka halarci jana’izar sun haɗa da tsohon ministan sufuri sanata Hadi Sirika da shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Katsina Alhaji Jabiru Salisu Tsauri.
An gudanar da jana’izar ne a fadan mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmummuni Kabir Usman.
Da kammala jana’izar sai gwamnan da sarkin Katsina tare da sauran mutane su ka taka zuwa maƙabartan ɗan takun inda aka binnne marigayi Talban Katsina.
