
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaban ƙasar Chadi, Mahamat Idriss Débu Itno ya karɓi baƙoncin babbar tawaga daga Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Mai bai wa shugaban ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu.
Lamarin ya auku ne a ranar Lahadi inda tawagar ta isar da saƙon Shugaba Bola Tinubu ga Shugaba Déby na jajenta masa game da harin da ƴan ta’adda suka kai a yankin Barkaram Island wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji da dama.
Shugaba Tinubu ya kuma jaddada goyon bayansa ga shugaban ƙasar.
Daga cikin mambobin tawagar akwai; Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa; Shugaban Sashin Leƙen asiri, Manjo Emmanuel Undiandeye da kuma Manjo Janar Ali Salau, Kwamandan jami’an haɗaka na MNJTF da wasu manyan jami’an tsaro.
Ganawar ta nuna yadda alaƙa tsakanin ƙasashen biyu ke da ƙarfi musamman wajen fuskantar ƙalubalen tsaro da shiyyarsu take fama da shi.
