
Daga BELLO A. BABAJI
Rundunar sojin sama ta Nijeriya (NAF), ta ce ta yi luguden wuta wa ƴan bindiga inda ta kashe da da yawa daga cikinsu har da shahararru biyu, wato Ɗan-Isuhu da Dogo Sule.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Kwamado Olusola Akinboyewa ya bayyana hakan cikin wata takarda a ranar Lahadi inda ya ce hakan wani ƙoƙari ne na tawagar atisayen ‘Fansar Yamma’ wanda jami’an suka gudanar a ranar Juma’a, 15 ga watan Nuwamba.
Lamarin ya auku ne a yankin ƙauyen Babban Ƙauye dake ƙaramar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.
Jami’in ya ce, wani bayani na sirri ya nuna cewa, ƴan bindigar na shirin kai hari ne ga jami’an tsaro da fararen hula a yankin Tsafe inda ba tare da jira ba, jami’an suka afka musu.
Ya kuma ce ƴan bindigar suna yawaita gudanar da ayyukansu na ta’addanci a ƙaramar hukumar waɗanda wani ɓangare na aiki ne ƙarƙashin jagorancin Ɗan-Isuhu da Dogo Sule.
