
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tafi birnin Rio de Janeiro na ƙasar Brazil don halartar taron shugabannin ƙasashen G20 da za a yi karo na 19.
An shirya gudanar da taron ne a ranakun 18 da 19 na watan Nuwamba inda za a tattauna muhimman batutuwa na ƙasa-da-ƙasa.
A cikin sanarwar da Mai taimaka wa Shugaba Tinubu kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce Shugaban ƙasar Brazil Inácio Lula da Silva ne ya aiko da saƙon gayyata ga shugaban na Nijeriya zuwa taron.
Taron zai haɗe shugabannin ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziƙi daga Nahiyoyin Afirka da Turai da kuma cibiyoyin kuɗi na ƙasa-da-ƙasa.
Wasu daga cikin ababen da za tattauna akwai batun magance matsalolin yunwa da talauci, gyare-gyare ga tsare-tsaren shugabanci da kuma hanyoyin amfani da nau’ukan ci-gaba na zamani.
