Duk mahalukin da ya tada tarzoma lokacin zaɓe a Kano ya kuka da kansa – DIG Hafiz

Daga RABIU SANUSI s Kano

Rundunar ‘Yan Sanda ta gargaɗi al’ummar Jihar Kano, musamman ‘yan siyasa da magoya bayansu a jihar da su ƙaurace wa dukkan wani yunƙuri na tada tarzoma yayin zaɓen gwamnoni da ‘yan majalisun jiha da ke tafe.

Muƙaddashin shugaban ‘yan sanda na ƙasa da zai kula da harkokin zaɓe a jihar, DIG Hafiz Muhammad Inuwa ne ya wannan garhaɗin yayin ganawarsa da shugabanin jami’iyyu da sauran masu ruwa da tsaki a jihar jim kaɗan bayan isowarsa.

DIG Hafiz ya ce haƙƙinsu ne da malaman addinai da masarautu da sauran masu ruwa da tsaki su nusar da al’ummar Kano batun zaman lafiya a lokacin wannan zaɓe da kuma bayansa a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

Ya ƙara da cewa, babu wani ɗan asalin Jihar Kano da zai ce baya son zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan jihar.

“Ba za mu yi ƙasa a gwuiwa ba wajen ɗaukar matakin da ya dace a kan duk wanda zai tada tarzoma a wannan zaɓe, don haka kowa ya shiga taitayinsa musamman mabiya siyasa.”

A cewarsa, cigaban Jihar Kano da ƙasar nan shi ne a gabansu madamar wani zai kawo wargi to za su ɗauki matakin hukunci a kansa.

Ɗaya daga cikin ‘yan takarar kujerar Gwamnan Jihar Kano ƙarƙashin jam’iyyar SDP, Hon Bala Muhammad Gwagwarwa, ya shaida wa manema labarai cewa ya ji daɗin wannan zama da aka yi.

Ɗa takarar ya tabbatar wa da DIG Hafiz cewa kowa ya san a batun tafiyarsa na siyasa ba ya ta’ammali da ‘yan daba, don haka ya ce zaman da aka yi zai ƙara taimaka masa.

Su ma a nasu jawaban, Sakataren Jam’iyyar APC na Jihar Kano, Ibrahim Zakari da Kakakin Jam’iyyar NNPP a jihar, Abdullahi Ibrahim Rogo, baki ɗaya sun yi na’am da matsayar rundunar ‘yan sanda da masu ruwa da tsaki. Tare da cewa, da alama zaɓe zai gudana cikin lumana.

Sun ce za su faɗakar da mabiyansu illar tada zaune tsaye tare da fahimtar da su Jihar Kano, jiharsu ce wadda ba su da kamar ta.