Duk wasu matakai na gyara harkar ilimi a jihar Kano Gwamna Abba na ɗauka – Bashir Baffa

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An bayyana cewa duk wani mataki da ya kamata a ɗauka na gyara ilimi, Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf zuwansa gwamnati ya na ɗauka sakamakon ya zo ya samu fannin a ragargaje da sai an yi da gaske. Allah ya kawo shi ya sa harkar cigaban ilimi a gaba fiye da komai ba don haka ba da ba a san yadda za a samu kai ba.

Babban Sakataren ma’aikatar ilimi na jihar Kano, Alhaji Bashir Baffa Muhammad ne ya shaida hakan ga manema labarai, ya ƙara da cewa yanzu a matsayinsu na ma’aikata su ya ragewa su riƙe masa amana, mutuƙar ilimin ya farfaɗo matasa da  ake ganinsu suna wasu abubuwa na rashin kyautawa za su daina su gina kyakkyawan cigaba na rayuwa.

Ya ce Kwamishinan ilimi mai barin gado, Haruna Doguwa ya yi rawar gani da ƙoƙari saboda mutum ne mai kaiwa da kawowa da son a yi tafiya tare da yake bada shawara a aiki da suka yi da shi tare, ya gyara masa aiki, tunda ya taras da shi a ma’aikatar.

Bashir Baffa ya ce a wajensa Umar Haruna ba tafiya ya yi ba tunda yana cikin gwamnati kuma yana ƙaunar cigaban ta da na jihar Kano kodayaushe suke buƙatar shawararsa za su je wajensa ya basu.

Babban Sakataren na ma’aikatar ilimi na jihar Kano ya ce suna alfahari da sabon Kwamishinan Ilimi da aka kawo musu Gwani Ali Haruna Makoɗa mutum ne aƙili mai jajircewa me aiki tuƙuru abu mafi girma Gwani na ƙur’ani da kishin jihar Kano da son cigaba, mutum ne mai haɗa kan ma’aikata a tafi tare.

Bashir Baffa Muhammad ya ce su da za su yi aiki ƙarƙashinsa za su ba shi haɗin kai saboda suna da manufar ganin cewa Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta cimma nasara a manufarta na gyaran ilimi da tasa a gaba.

A ranar Laraba ne dai Dokta Gwani Ali Haruna Makoɗa ya fara aiki a matsayin sabon kwamishinan ilimi na jihar Kano a hukumance, inda ya yi alƙawarin ƙara ɓullo da wasu shirye-shirye da nufin bunƙasa fannin ilimi a jihar.

By ukarofi