Shugaban majalisar wakilai, Tajuddeen Abbas ya goyi bayan ƙudurin dokar haraji 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya ce ƙarancin harajin da Nijeriya ke samu ya kasance wani babban cikas ga ci gaban ƙasar.

Abbas ya bayyana haka ne a wajen gabatar da ƙudurin kasafin kuɗin 2025 ga wani zama na haɗin gwiwa na majalisun tarayya da Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi a Abuja ranar Laraba.

A cewarsa, rabon harajin Nijeriya zuwa kayan da ake samarwa a ƙasa, GDP, a halin yanzu ya yi ƙaranci da kusan kashi 10.9 cikin 100 a 2024, inda ya ce yana cikin mafi ƙaranci a Afirka, wanda ya yi ƙasa da matsakaicin mataki na  nahiyar wanda ya ke a kashi 15.6 cikin ɗari.

Ya ce yawan kuɗin da ake tara harajin ɓAT a Nijeriya a kusan kashi 20 cikin 100 ya yi ƙasa da kusan kashi 70 cikin 100 da ƙasashen Afirka ta Kudu, Eƙuatorial Guinea da Zambia suka samu.

Abbas ya ce, tunkarar waɗannan ƙalubale na buƙatar sauye-sauyen manufofin haraji cikin gaggawa, don faɗaɗa tushen harajin ƙasar, da inganta bin ƙa’ida, daidaita harkokin gudanarwa, da kuma rage dogaro da karɓar bashi.

Ya ce ‘yan majalisar za su ci gaba da yin aiki tare da gwamnatin Tinubu don ganin an yi gyare-gyaren da ya kamata, kuma mai inganci da kuma la’akari da buƙatun marasa galihu.

By ukarofi