Duniya ba ta buƙatar duk wani nau’i na yaƙin cacar baka

Daga SAMINU HASSAN

A baya bayan nan, yayin zaman kwamitin tsaro na MƊD game da rikicin ƙasar Ukraine, an tabo muhimman batutuwa game da halin da ake ciki, don gane da wannan rikici da ya ki ci ya ki cinyewa, wanda a yanzu haka ya doshi wata na 7.

Tuni sassan duniya daban daban suka dandani raɗaɗin tasirin wannan rikici, kama daga kamfa, da hauhawar farashin makamashi a sassan nahiyar Turai, zuwa ƙarancin hatsi, da takin zamani da sassan ƙasashe masu tasowa, kamar nahiyar Afirka ke fama da shi.

Game da wannan batu, tsagin ƙasar Sin na ganin a wannan gaba da duniya ke fuskantar manyan ƙalubale, ciki har da yunƙurin farfaɗowa daga tasirin annobar COVID-19, ba wata ƙasa a duniya dake fatan sake fuskantar yakin cacar baka.

Hakan na nufin ƙasar Sin ba ta gamsu da yadda wasu ƙasashen duniya, musamman masu ƙarfin faɗa a ji ke ƙara rura wutar rikice-rikice, da haifar da saɓani a sassan duniya daban daban ba.

Kazalika matakin ƙungiyar tsaro ta NATO, na ƙara faɗaɗa tasirinta zuwa gabashin duniya, bai haifar da komai ba illa fito na fito da rura wutar rikici.

Ƙasar Sin ta gamsu cewa, yanayin matsi da ci gaban duniya ke fuskanta, ya wajabta yin taka tsantsan, da zage damtse, wajen ganin an kawar da rarrabuwar kawuna, da kauce wa rikici tsakanin sassan ƙasa da ƙasa.

Irin yadda ƙasashe masu tasowa suke fama da kamfar hatsi sakamakon rikicin Rasha da Ukraine, ya nuna cewa, zaman lafiyar wasu yankunan duniya, na iya yin babban tasiri ga sauran yankuna, kuma abu mafi dacewa shi ne sassan ƙasa da kasa su yi haɗin gwiwa da juna, wajen kawo ƙarshen duk wasu matakai na rura wutar cacar baka, wadda sau da yawa ke kaiwa ga ɓarkewar tashe-tashen hankula.