Xi ya aike da wasiƙar taya murna ga taron haɗin gwiwar kafofin watsa labarai tsakanin Sin da Afirka karo na biyar

Daga CMG HAUSA

Yau ne, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasiƙar taya murna ga taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar kafofin watsa labarai tsakanin Sin da Afirka karo na 5.

Xi Jinping ya yi nuni da cewa, tun bayan kafa shi shekaru 10 da suka gabata, dandalin ya samar da wata muhimmiyar kafa ga kafofin watsa labaru na Sin da Afirka, wajen inganta tattaunawa da haɗin gwiwa, kana ya taka muhimmiyar rawa wajen sa ƙaimi ga yin musaya da yin koyi da juna, tsakanin wayewar kan Sin da Afirka, da zurfafa cikakkiyar dangantakar haɗin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin ƙasashen biyu.

Shugaba Xi ya kuma bayyana fatan cewa, kafofin watsa labaru na ƙasashen Sin da Afirka, za su ci gaba da tabbatar da zumunci da haɗin gwiwa tsakanin sassan biyu, da ƙoƙarin zama masu sa ƙaimi ga yin musayar al’adu da al’ummomi, masu kiyaye gaskiya da adalci, da bunƙasa ci gaban duniya, ta yadda za a ba da labarin ƙasar Sin da kasashen Afirka a sabon zamani, da yaɗa dabi’un bai ɗaya na dukkan bil-Adama, da ba da gudummawar hikima da ƙarfafa gwiwa wajen inganta gina al’umma mai makomar bai daya ga ɗaukacin bil-Adama.

Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa