Jarin Sin ya taimaka wajen raya tsarin samar da kayayyaki a Afrika

Daga CMG HAUSA

Majalisar kula da harkokin kasuwanci tsakanin Sin da Afrika (CABC), ta fitar da wani sabon rahoto kan jarin da ƙasar Sin ta zuba a ƙasashen Afrika, wanda ya bayyana cewa, cikin shekaru 22 da suka gabata, ɓangarorin biyu sun samu dimbin nasarori ta kowacce fuska tare da haɗa gwiwa a bangarori da dama.

Rahoton da aka fitar a jiya, ya ce manyan jami’an majalisar sun ce kamfanonin ƙasar Sin sun yi kyakkyawan tasiri, kana sun kasance wani ɓangare mai matuƙar amfani na kasuwar Afrika.

Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa