Kungiyar ƙasashen yammmacin nahiyar Afrika, ECOWAS ta caccaki hare-haren da ƴan ta’adda su ka kai babban birnin Mali, Bamako a ranar Talata.
A wata sanarwa, ECOWAS ta bayyana rashin jin daɗin ta a game da waɗannan hare-hare, waɗanda ta ce su na barazana ga zaman lafiyar yankin yammacin nahiyar Afrika.
Sanarwar ta ƙara da cewa ƙungiyar tana jaddada ƙudirinta a kan duk wani shiri da kawo zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.
A ranar Talata ce aka kai wa birnin Bamako munanan hare-hare, waɗanda ƙungiyyar nan mai iƙirarin jihadi da ke da alaƙa da Al-ƙaeda ta ɗauki alhakin kaiwa. Har yanzu dai ba a bayyana adadin mutanen da waɗannan hare-hare suka rutsa da su ba.
Birnin Bamako bai cika fuskantar hare-hare na masu iƙirarin jihadi ba kamar yadda wasu sassan ƙasar ke fuskanta kusan kullayaumin.
