Mutumin da ake zargi da hayar mutane domin yiwa matarsa fyaɗe a ƙasar Faransa, Dominique Pelicot ya nemi gafarar jama’a, ya yin da shima ya bayyana kansa a matsayin mai aikata laifin fyaɗen.
Pelicot mai shekaru 71 ya faɗa komar ‘yan sanda ne lokacin da aka kama shi saboda zargin hayar mutane ta kafar intanet domin zuwa su ci zarafin matarsa ta hanyar fyaɗe.
Bayanan ‘yan sanda sun ce wanda ake zargin na bai wa matar tasa sinadarin da zai kawar da hankalinta ne kafin sanya baƙin da ya ɗauko yin lalata da ita.
Yayin da yake amsa tambayoyi a gaban kotu a ranar Talata, Pelicot ya ce babu bambanci tsakaninsa da sauran mutane 50 da ya sa suka yiwa iyalin nasa fyaɗe, saboda haka yana neman gafara daga wurinta.
Wanda ake zargin ya ce duk waɗanda ya ɗauko hayarsu domin lalata da matar tasa sun san cewa fyaɗe za su yi, kuma ya yi nadamar laifin da ya aikata.
Uwargidan Pelicot, Gisele ta buƙaci a gudanar da shari’ar a bainar jama’a domin kowa ya san abinda ya faru da kuma irin matakan da suka dace a ɗauka domin kare haƙƙin mata.
Daga cikin tuhume tuhumen da ake yiwa Pelicot harda kwashe shekaru kusan 9 tsakanin shekarar 2011 zuwa 2020 na sanya mata sinadarin da ke kawar mata da hankali domin bada damar yi mata fyaɗen a ƙauyen Mazan da ke ƙasar ta Faransa.
