Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da wasu makusantan tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar sun yi ganawa ta musamman da shugabannin jam’iyyar SDP.
Wannan ganawa ya zo be a daidai ana raɗe-raɗin yiwuwar sauya sheƙarsa daga APC zuwa wata jam’iyya, zancen da tsohon gwamnan ya musanta a farkon wannan makon.
A ranar Laraba, El-Rufai da Otunba Segun Showunmi, tsohon kakakin Atiku da kuma Hamza Almustapha suka ziyarci jam’iyyar SDP a Abuja.
Ko da ya ke ba a faɗi dalilin wannan ziyara ba, masu fashin baƙi na yi masa da yiwuwar tsunduma jam’iyyar domin fafatawa da gwamnati mai ci.