
Daga FAROUK ABBAS
Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i ya karbi baƙuncin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a gidansa da ke Abuja a ranar Alhamis, kwanaki kaɗan bayan kai wa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ziyara a Daura, Jihar Katsina.
A ƴan kwanakin nan ne El-Rufa’i na jam’iyyar APC, ya yi ta ganawa abokanan hamayyarsu na siyasa ciki har da ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da kuma ziyartar shugaban jam’iyyar SDP na ƙasa a Abuja da ya yi.
El-Rufa’i, wanda tsohon ministan Abuja ne, na ɗaya daga cikin waɗanda aka zaɓa za a basu muƙaman ministoci a gwamnatin shugaba Tinubu, wanda hakan bai samu ba daga baya kasancewar Majalisar Dattijai bata tantance shi ba kan lamurran tsaro.
Kwanan nan tsohon ministan ya je ƙasar waje inda ya bayyana ficewarsa daga harkokin siyasa, amma bayan dawowarsa, ya kai ziyara sakatariyar SDP wanda hakan ya janyo cecekuce a cikin al’umma.
Shehu Sani, tsohon Sanata ne da ya wakilci Jihar Kaduna ta tsakiya inda ya ce ziyarar da wasu sanannun ƴan siyasa ke kai wa Buhari na da alaƙa da shirin su na sauke Tinubu a zaɓen shekarar 2027.
