Dogo Giɗe na ba manoma kariya a Zamfara

Spread the love

Mazauna garin Magami dake ƙaramar hukumar Gusau sun yi murna sosai saboda dawowar Dogo Giɗe wannan yankin.

Giɗe ya ba yan garin umarnin su koma gonakin su ba tare da tsoron wani zai kama su ba. Dogo Giɗe shine shahararen ɗan bindigar nan, wanda dashi a cikin wanda suka sace yara yan makaranta na garin Kuriga dake jihar Kaduna.

Bayan artabun shi da sojoji, Giɗe ya dawo wani gari da ake kira Kizara, wanda yake gabashin Magami. A nan ne yace mutane su koma gonakin su zai basu kariya.

By ukarofi