EndSars: An gudanar da zanga-zangar tunawa da kisan Lekki a Legas

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A jiya Alhamis ne wasu ɗaruruwan mutane suka gudanar da zanga-zangar jimamin tunawa da kashe ‘yan uwansu da suke zargin jam’ian tsaro sun yi a Ƙofar Lekki shekaru biyu da suka gabata a zanga-zangar ƙin jinin ‘yan sandan SARS.

Sai dai jami’an rundunar ‘yan sandan jihar ta Legas sun ta harba barkonon tsohuwa kan masu zanga-zangar da nufin daƙile shirinsu.

Masu zanga-zangar dai sun yi tattaki ne a kan ƙofar a wani ɓangare na bukukuwan tunawa da zagayowar ranar, an ce sun yi arangama da ‘yan sandan da ke ɗauke da makamai da aka tura domin kare tarzoma.

Fitattun jarumai da suka haɗa da Folarin Falana, mawakin Nijeriya da aka fi sani da Falz ne su ka jagoranci wannan fitar jiya Alhamis.

A cewar sanarwar da a ka raba wa manema labarai, motocin da ke jerin gwanon za su bi ta ƙofar karɓar haraji, suna ɗaga tutocin Nijeriya tare da rera taken #EndSARS.