Kotu ta bada umarnin bincikar shugabannin hukumomin tsara birane da na kadarorin Gwamnatin Kano

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Wata babbar kotu a Jihar Kano ta bai wa kwamishinan ‘yan sandan jihar umurnin su binciki Shugaban Hukumar Tsara Birane, Abdulwahab da na Kula da Kadarorin Gwamnati na Jihar Jibrilla Muhammad bisa zargin da ake musu na ruguje wa ‘yan kasuwar Bampai shagunansu da yin awon gaba da kayayyakinsu ba tare da sahalewar doka ba.

Lauyan ‘yan kasuwar Barista Abba Hikima Fagge ya bayyana hakan yayin da yake ƙarin haske ga manema labarai, inda ya ce wannan ya biyo bayan ƙunshin tuhuma da suka kai wa kotun.

Ya ce kotun ta baiwa kwamishinan ‘yan sanda umarnin ya tuhume su wanda shi ma doka yake wa aiki kuma zaman dokar yake kuma suna yi masa kyakkyawan zato zai yi abinda ya dace.

Barisata Abba, ya ce, “idan ka ruguje wa mutum wuri ka ɗauke masa ƙofofinsa da kwanuka wannan laifi ne, idan ka ruguje abu bayan an ce kar ka ruguje laifi ne, haka in ka zo ka shiga wajen mutum tunda da kayansa a ciki ka ruguje laifi ne.”

Tun farko dai kotu ta bada umurnin kada waɗannan hukumomi su rushe kasuwar sai an saurari shari’ar da take tsakaninsu da ‘yan kasuwar, amma sai suka yi biris da umurnin kotun da ake ganin hakan a matsayin tsabagen raini ne ga doka.

Barista Abba Fagge ya ce, “odar da aka samu yanzu na a tuhumi hukumomin alaƙarta ‘yar kaɗan ce da ta ƙin bin umurni da suka yi wannan zargi ne suke musu na yin laifi da za a iya kama mutum a kai shi gidan yari.

Wancan kuma laifi ne suka yi wa kotu na ƙin bin umurninta wanda wannan shi ma yana nan kotu ita za ta yi hukuncin saɓa umurninta da aka yi.”