Makarantar Almumtaz ta yi bikin yaye ɗaliban ta karo na biyar

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Makarantar Al’mumtaz dake kusa da masallacin Idi dake kan tsohuwar hanyar Nasarawa a garin Keffi, Jihar Nasarawa, ta yi bikin yaye ɗalibanta da suka kammala karatun Alƙur’ani da na zamani karo na 5 tare da karrama su da ba su kyaututtuka da sauransu. 

Bikin wanda aka gudanar a harabar makarantar ya samu halarcin iyayen ɗaliban da ‘yan siyasa da sarakunan gargajiya da sauran shugabanni a duka matakai. 

A jawabin shugaban makarantar kuma Darakta Dr. Musa Ahmad Isa ya faro ne da bayyana taƙaitaccen tarihin makarantar ta Al’mumtaz wanda a cewarsa aka kafa ne da nufin inganta tare da aiwatar da wa’azuzzukan Manzon tsira Muhammadu SAW a idon duniya gabaɗaya.

Kuma tun bayan kafa makarantan mahukuntan makarantar na cigaba da aiki tuƙuru don cimma burin musamman ta samar wa ɗaliban su ingantaccen ilimin addinin Musulunci da na zamani. 

Ya ce kawo yanzu makarantar ta yaye ɗalibai da dama da suka kasance nagari masu kyakkyawar tarbiyya da bin tafarkin Ubangiji a inda suke a yayin da suke kuma bai da gagarumin gudunmawa wajen ɗaukaka sunnar Ma’aiki da cigaban ƙasa bakiɗaya. 

A cewarsa bayan waɗannan akwai kuma wasu nasarori da dama da makarantar ta Al’mumtaz ta cimma kawo yanzu da suka haɗa da samar da ingantattun kayayyakin karatu musamman na’urorin kwamfuta da sauran su duk na zamani don inganta yanayin karatu a makarantar. 

Dr. Musa Ahmad Isa ya kuma yi amfani da damar inda ya gode wa iyayen yara da malaman makarantar dangane da hain kai da suke bai wa hukumar gudanarwar makarantan kawo yanzu inda ya kuma buƙaci iyayen su riƙa biyan kuɗaɗen makarantan ‘ya’yan su da sauran nauyi dake wuyan su don bai wa makarantar damar cigaba da samar wa ‘ya’yan nasu ingantaccen ilimin. 

A nasu ɓangaren sauran manyan baƙi da suka halarci bikin suka kuma yi jawabi da suka haɗa da maimartaba Sarkin Keffi Alhaji Shehu Chindo Yamusa na III da Ƙaramin Ministan Ma’aikatar Ayyuka na Ƙasa Alhaji Umar El-Yakub da jiga-jigan ‘yan siyasa da sauran su duk sun yaba wa mahukuntan makaratar ta Al’mumtaz game gagarumin gudunmawa da suka bayar kawo yanzu dake cigaba da ɗaukaka addinin Musulunci da na zamani, inda suka buƙace su su cigaba da haka. 

Sauran abubuwa da aka gudanar a wajen bikin mai ɗimbin tarihi sun haɗa da bai wa ɗaliban kyaututtukan yabo daban-daban da gabatar da jawabai da lakca-lakca da karatun Alƙur’ani kaitsaye da sauran su.