Xi ya jaddada fa’idar babban taron wakilan JKS na 20

Daga CMG HAUSA

Yau ne, babban sakataren Jam’iyyar Kwaminis ta ƙasar Sin Xi Jinping, da sauran mambobin zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS karo na 20 da suka haɗa da Li Qiang da Zhao Leji, da Wang Huning, da Cai Qi, da Ding Xuexiang da Li Xi, suka bayyana a gaban ‘yan jaridu a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing, fadar mulkin ƙasar Sin.

Babban sakataren kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta ƙasar Sin Xi Jinping, ya bayyana cewa, babban taron wakilan JKS na karo na 20, shi ne babban taro na ƙara ɗaga tutar jam’iyyar, da haɗa ƙarfi da ƙarfe, da inganta haɗin kai da kuma sadaukarwa.

Xi ya bayyana cewa, ya kamata jam’iyyar ta yi wa jama’a aiki ta kuma dogara ga jama’a a kan tafiyar da aka sanya a gaba.

Xi ya ce, ya kamata jam’iyyar ta ci gaba da yi wa kanta gyare-gyare kan wannan tafiya da aka sanya a gaba. Yana mai cewa, ƙasar Sin za ta kara buɗe kofarta ga ƙasashen ƙetare, da sa kaimi ga zurfafa yin gyare-gyare a gida da buɗe ƙofa ga waje a dukkan fannoni.

Ya ƙara da cewa, za mu yi aiki da sauran al’ummomin ƙasashe, don ɗaukaka dabi’un bil-Adama na zaman lafiya, da bunkasuwa, da nuna adalci, da demokuraɗiyya da ‘yanci, da kiyaye zaman lafiya a duniya, da bunƙasa ci gaban duniya, da ci gaba da gina al’umma mai makomar bai ɗaya ga ɗaukacin bil-Adama.

Mai fassara: Ibrahim