Faɗan daba ya yi sanadiyyar rasuwar mutane biyu a Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar mutane biyu biyo bayan faɗan daba da ake zargin wasu matasa daga unguwannin Zango da kuma Ƙofar Mata.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan a zantawarsa da manema labarai a hedikwatar rundunar da ke unguwar Bompai Kano.

SP Abdullahi Kiyawa ya ce tun a ranar Lahadi, suka samu kiraye-kiraye daga unguwar Ƙofar Mata daidai lokacin da aka tashi wasa a filin wasa na Sani Abacha Stadium, inda wasu matasa suka dinga yin faɗace-faɗacen daba tsakanin Unguwa da Unguwa.

Kiyawa ya ce “Bisa rahotannin da muka samu an ce mana faɗan daba ne tsakanin unguwar Zango da kuma Ƙofar Mata”

“Bayan Samun rahotanni marasa daɗi,kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano, CP Salman Dogo Garba ya tura dakarun ‘yan Sanda da gaggawa wajen da lamarin ya faru , kuma sun samun rahotan mutuwar mutane biyu.

Rundunar ta ce yanzu haka ta duƙufa wajen gudanar da bincike don ganin duk wanda yake da hannu akan faɗace-faɗacen dabar, ya zo don ya fuskanci hukunci”. cewar Abdullahi Kiyawa,

Kazalika, Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa a yau Litinin rundunar ta ƙara tura dakarun ‘yan sanda, bayan samun wasu kiraye-kirayen don ganin an yi abin da yakamata don wanzar da zaman lafiya.

Daga nan rundunar ta ja hankalin al’umma, musamman wajen taimaka wa jami’an ‘yan sanda da bayanan sirri tunda dai waɗanda suke aikata laifukan yan unguwa ne.

By ukarofi