Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da wani gagarumin shiri na farfaɗo da masana’antar auduga a Najeriya, da nufin samar da ayyukan yi sama da miliyan 1.4 a duk shekara a fannin.
A cewar wata sanarwa da ta fito daga ofishin mataimakin shugaban ƙasar Kashim Shettima, shirin na haɗin gwiwa ne tsakanin gwamnati da kwamitin ba da shawara kan auduga (ICAC).
Da yake jawabi a wajen wani taro da jami’an ICAC, mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ya jaddada buƙatar ganin masu ruwa da tsaki sun haɗa kai don bunƙasa darajar auduga a fannonin da suka haɗa da noma, saka, ciyawa, da murza auduga.
Matakin wani ɓangare ne na yunƙurin gwamnati na samar da masana’antu, da nufin samar da damammakin aiki a fannin sana’ar auduga.
Gwamnonin jihohin Legas da Imo da suka halarci taron, sun nuna goyon bayansu ga shirin tare da yin alƙawarin haɗa kai da masu ruwa da tsaki domin bunƙasa fannin.
ICAC ta yi alƙawarin bayar da shawarwari na ƙwararru da goyan baya don haɓaka yawan aiki da dawo da kimar masana’antun audiga da sauƙaƙe saka hannun jari a fannin
Ana sa ran farfaɗo da masana’antar auduga zai yi tasiri sosai ga tattalin arzikin Najeriya da samar da ayyukan yi da ma kawo sauyin tattalin arziki.
