Sanata Ndume ya ba jami’iyyar APC haƙuri a kan sukar gwamnatin Tinubu

Spread the love

Tsohon bulaliyan Majalisar Dattijai, Sanata Ali Ndume ya ba shugabancin jam’iyyar APC mai mulki haƙuri saboda rashin tuntuɓar jam’iyyar kafin yayi zargin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da rashin kyakkyawan shugabanci.

Ndume wanda ke wakiltar Kudancin Borno a majalisar dattijai, duk da haka ya ce yana nan kan bakarsa, yana jaddada cewa duk abin da ya faɗa ko ya aikata ya fito ne daga kishin ƙasa.

“Jiya jam’iyya ta gayyace ni kuma ga ni a nan don mu tattauna abubuwa game da abin da ya faru wanda kowa ya sani, haƙiƙa shugaban jam’iyya ba wai kawai shugaban jam’iyya bane a gare ni amma uba ne,” inji ɗan majalisar.

“Ba abin mamaki bane cewa an gayyace ni don jin nawa ɓangaren kuma munyi tattaunawa na cikin gida. Na amince da kuskuren rashin magana da jam’iyya a matsayin mataki na ƙarshe, kuma na yiwa jam’iyya alƙawarin cewa dukkanin ƙorafe-korafena zan kawo wa jami’iyya.

Sanatan an cire shi kuma an maye gurbinsa da Sanata Mohammed Monguno bayan wata wasiƙa daga jam’iyyar mai mulki don hukunta ɗan majalisar saboda maganganunsa masu zafi da rashin kulawa game da Shugaban ƙasa.

A cikin wasikar da shugaban jam’iyya na ƙasa, Abdullahi Ganduje da sakataren jam’iyya na kasa, Sanata Ajibola Basiru suka sanyawa hannu tare, jam’iyyar ta umurci majalisar dattijai da ta hukunta dan majalisar, kasancewarsa babban jagora na jam’iyyar.

By ukarofi