Farfesa Sa’adatu ta cimma ɗimbin nasarori a shekara guda, inji Kwamaret Ja’afar 

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya 

Shugaban Sashin Hulɗa da Jama’a na Babban Jami’ar Gwamnatin jihar Nasarawa da aka fi sani da NSUK a Turance da ke garin Keffi a ƙaramar Hukumar Keffi, Kwamaret Ja’afar Abdullahi Abubakar ya yaba wa shugabar jami’ar Farfesa Sa’adatu Hassan Liman dangane da cimma ɗimbin nasarori da suka ma wuce mitsali a cikin shekara guda kacal da tayi akan mulkin shugabancin jami’ar zuwa yau.

Mai magana da yawun jami’ar kwamaret Ja’afar Abdullahi Abubakar ya bayyana haka ne a lokacin da yake zanta da wakilin mu a ofishin sa da ke babban ginin jami’ar a mako da ake ciki game da kamun ludayin farfesar kawo yanzu cikin shekara guda.

Ya ce, tabbas dole ne a yaba wa farfesa Sa’adatu Hassan Liman idan akayi la’akari da ire-iren sabbin tsare-tsare da shirye-shirye da ayukan cigaba da tayi ta aiwatar cikin shekara daya kacal da tayi a kujerar waɗanda yace sun haɗa da sabbin gine-gine da ingata yanayin karatu da koyarwa da hulɗa da manyan abokan aiki daga ciki da wajen ƙasar nan da jin daɗin ma’aikata da malamai da dalibai da sauran su musamman uwa uba batun rage ko kawo aarshen bacaka da dukiyar jami’ar da sauran su saɓanin yadda lamarin yake a da.

Kwamaret Ja’afar Abdullahi Abubakar ya ƙara da cewa a yanzu duka fannonin jami’ar suna aiki tare batareda wasu matsaloli ba tunda farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta hau ragamar shugabancin jami’ar ta NSUK shekara guda.

Ya taya ta murnar cika shekara gudan inda yayi fatar Allah ya kara mata lafiya da basirar cigaba da gudanar da shugabani nagari wa jami’ar dama jihar baki ɗaya.

Shugaban sashin hulda da jama’a na jami’ar Jaafar Abdullahi Abubakar ya cigaba da bayyana cewa “Shiyasa nake so inyi amfani da damar nan in mika fatar alherin mu na musamman muna a madadin duka ma’aikatan sashin nan na hulda da jama’a zuwa ga shugabarmu adala wato farfesa Sa’adatu Hassan Liman game da wadannan dinbin nasarori dana bayyana maka cewa ta iya cimma da yardar Allahi cikin shekara 1 kacal da tayi sa’anan muna fatar sauran shugabannin mu a duka matakai zasu cigaba da yin koyi da ita.”   

Wakilinmu a jihar JOHN D. WADA dai ya gano cewa shugabar jami’ar farfesa Sa’adatu Hassan Liman dai ta fara aiki ne a matsayin shugabar jami’ar a watan Afrelun shekarar 2024 da ya gabata inda a yanzu haka ta cika shekara guda kenan a kujerar.

By ukarofi